Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya

Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya

A karon farko PDP ta nada matashi mai shekaru 25 Mohammad Kadade Suleiman, a matsayin sabon shugaban matasan jam'iyyar ta adawa, lamarin ya kuma haifar da cece-kuce.

Daga cikin bukukuwan da suka gudana a taron gangamin PDP, an kada kuri'u na kujeru daban-daban na shugabancin jam'iyyar ta adawa.

Legit.ng Hausa ta ruwaito a baya cewa, PDP ta yi sabbin kujerun shugabancin jam'iyyar, inda aka lissafo wasu jami'an PDP 21 da suka yi nasara a zaben.

Bayan zaben, an samu cece-kuce daga bangarori daban-daban na 'yan Najeriya, inda jama'a da yawa suka bayyana ra'ayoyinsu game da hakan.

Dan Shekara 25 a matsayin shugaban matasan PDP: Martanin 'yan Najeriya
Matashin da ya lashe zaben shugaban matasan PDP | Hoto: Adamu Umar Chiroma
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karo na biyu, Legit.ng Hausa ta sake tattaro martani da ra'ayoyin jama'a kan wannan gagarumin lamari.

Kara karanta wannan

Cikin hotuna: Matashi mai shekaru 25 da ya lashe kujerar shugaban matasan PDP

Da yake mayar da martani kan wannan lamari, babban daraktan kungiyar Platform for Youth and Women Development (PYWD), Kingdom Ogoegbunam, ya taya Suleiman murnar fitowar a a matsayin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa.

A cewarsa:

“Haka (nasarar Suleiman) abin farin ciki ne, bai taba faruwa a tarihin kowace jam’iyya mai mulki a Nijeriya ba, don haka ina yaba wa jam’iyyar PDP da ta ba da damar shigar matasa, kuma tabbas wannan wani tsani ne ga matasan Najeriya su zage damtse su shiga siyasa."

Ya kuma ce, hakan zai taimaka sosai wajen shigar matasa a harkokin siyasa, wanda a cewarsa zai ba da kwarin gwiwa ga matasan da ke son ci gaban Najeriya.

A bangare guda, Habib Sunusi yace:

"Tabbas PDP Ta Shirya Yaudarar Yan Nigeria Musamman Mu Matasa Tana so Tayi Amfani Damu."

Wilson Ejiofor Ubazi yace:

"Yanzu kuka iso. Cire wadannan tsofaffin kuraye wadanda ba su son ci gaban jam’iyyar, shi ne hanya mafi dacewa ta kawo ci gaba. Da wadannan sabbin membobin gaba daya, za su yi aiki da karfi don cimma nasara. Da fatan za su yi."

Kara karanta wannan

Bayan lashe zabe, sabon shugaban PDP ya mika zazzafan sako ga jam'iyyar APC

Inimfon Atat ya ce:

"Wannan abin a yaba ne sosai kuma na hori jam’iyyar da ta yi aiki tukuru don samun mulki a 2023."

Nuhu Omuya Suleiman Mohammed ya ce:

"Duk da haka APC za ta ci nasara a kan PDP a zaben 2023, ku shaida batu na..."

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a nasa bangaren ya ce:

"Daya daga cikin manyan abubuwan da suka faru a taron gangamin PDP na jiya shine zaben Mohammed Kadede Suleiman mai shekaru 25 a matsayin shugaban matasa na kasa mai jiran gado na jam'iyyar PDP.
"Wannan ne ya sa a safiyar yau na yi farin ciki da tarbar zababben shugaban matasan jam’iyyar PDP a gidana da ke Abuja, inda ya zo ya yi mana godiya bisa goyon bayan da muka ba shi.
"A wajen taron, na jaddada cewa, a yayin da yake shirye-shiryen hada ’yan Najeriya da yawa zuwa jam’iyyarmu, zan kasance a shirye in ba shi goyon baya. Sa'a Muhammad!

Kara karanta wannan

Tsohon minista ya bayyana abubuwa 7 da ya dace PDP ta yi don ganin karshen APC a Najeriya

Cikin hotuna: Matashi mai shekaru 25 da ya lashe kujerar shugaban matasan PDP

A wani labarin, rahotanni da muke samu daga jaridar Punch sun bayyana cewa, wani dan shekara 25 ne ya zama shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa.

An zabi Mohammad Kadade Suleiman mai shekaru 25 a matsayin shugaban matasan jam'iyyar PDP na kasa.

An zabe shi ne a babban taron jam’iyyar na kasa da aka kammala a Abuja. A jiya Asabar ne aka gudunar da taron gangamin PDP, taron da ya sami halartar jiga-jigan jam'iyyar ta PDP daga sassa daban-daban na kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel