Shugabanci a 2023: Shugaban APC Buni da tawagarsa sun ziyarci Tinubu a gidansa

Shugabanci a 2023: Shugaban APC Buni da tawagarsa sun ziyarci Tinubu a gidansa

  • Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya tarbi tawagar jam'iyyar a gidansa
  • Shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC mai mulki kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya jagoranci tawagar
  • Kwanan nan Tinubu ya dawo Najeriya bayan ya shafe watanni uku a London don jinya da hutawa

Legas - Alamu sun nuna burin zama shugaban kasa na jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya samu babban ci gaba a ranar Lahadi, 24 ga watan Oktoba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan karin darajar cewa bai rasa nasaba da ziyarar shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC mai mulki kuma gwamnan jihar Yobe ba, Mai Mala Buni, da tawagarsa ga tsohon gwamnan na Legas.

Tawagar Buni, don haka, ta shiga cikin manyan shugabannin APC da suka ziyarci Tinubu a London da Legas a cikin watanni uku da suka gabata.

Kara karanta wannan

2023: Jihar Kano a shirye take ta goyi bayan burin Tinubu a shugabancin Najeriya, kakakin majalisa

2023: Hotunan shugaban APC Buni da tawagarsa yayin da suka ziyarci Tinubu a gidansa
Gwamnan jihar Yobe Buni, Da jagoran APC, Tinubu | Hoto: Oluomo Segun Olulade
Asali: Facebook

Tinubu ya tafi Landan don a yi masa tiyata a gwiwoyinsa, lamarin da ya nisanta shi daga bainar jama'a na tsawon watanni uku.

Kungiyoyi da jiga-jigan 'yan siyasa na ci gaba da nuna goyon bayansu ga Bola Tinubu gabanin isowar zaben shekarar 2023 mai zuwa.

A wannan ziyarar, ba a bayyana abubuwan da aka tattauna akansu ba, amma ana kyautata zaton batu ne da ke da alaka da tsayawa takarar shugabanci a zaben na 2023.

2023: Jihar Kano a shirye take ta goyi bayan burin Tinubu a shugabancin Najeriya, kakakin majalisa

Biyo bayan jita-jitar burin takarar shugaban kasa na jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Hamisu Chidari, yayi babbar magana.

Legit.ng ta rahoto cewa ya ce APC a jihar Kano za ta goyi bayan Tinubu idan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo

Chidari ya yi magana ne a wajen kaddamar da kungiyar goyon bayan Tinubu (TSG) da kwamitocin gudanarwa na kungiyar a Abuja ranar Asabar, 23 ga watan Oktoba.

Matasan Arewa sun nemi jam'iyyun siyasa su ba Tinubu tikitin shugabanci a 2023

Wata kungiyar Arewa mai suna Arewa Youth Alliance for 2023, ta bayyana goyon baya ga tsohon gwamnan jihar Legas kuma Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu a matsayin mafi kyawun dan takarar shugaban kasa a 2023.

Kungiyar ta bukaci dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya da su fara shirin daukar Tinubu a matsayin dan takara daya tilo a Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel