Dubbannin mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa Jam'iyyar PDP a wannan jihar

Dubbannin mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa Jam'iyyar PDP a wannan jihar

  • Jiga-jigai da kuma mambobin jam'iyyar APC sama da 5,000 ne suka sauya sheƙa zuwa PDP a jihar Cross Ribas
  • Shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar, Venatius Ikem, shine ya tarbi masu sauya sheƙar a wurin taron da aka shirya musu na musamman
  • Ikem yace an jima ba'a yi taro da aka haɗa dandazon yan jam'iyya ba a mazaɓar Cross Ribas ta Arewa kamar yadda mutane suka tattaru a wurin taron

Cross River - Shugaban jam'iyyar hamayya PDP reshen jihar Cross Ribas, Venatius Ikem, ya karbi masu sauya sheƙa sama da mutun 5,000 daga APC zuwa PDP.

Vanguard ta ruwaito cewa PDP ta shirya taron karɓar dubbannin masu sauya shekan ne a kwalejin fasaha dake Ogoja.

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban PDP yace dawowar tsofaffin yan PDP da kuma sauya shekar wasu, wata alama ce ta nasarar da jam'iyyar ke fatan samu a zaɓen dake tafe.

Kara karanta wannan

Yan jam'iyyar APC akalla 1000 sun kona tsintsiya a jihar Bauchi, sun koma PDP

Jam'iyyar PDP
Dubbannin mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa Jam'iyyar PDP a wannan jihar Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Rahoto ya bayyana cewa tsaffin mambobin PDP da suka sake komawa, da kuma sabbin da suka shigo, sun fito ne daga kananan hukumomi 5 dake jihar Cross Ribas.

Suwaye manyan yan siyasan da suka koma PDP?

Daga cikin jiga-jigan yan siyasan da suka koma PDP, har da tsohon mashawarci na musamman ga tsohon gwamnan jihar, Dakta Peter Oti.

Shugaban PDP ɗin ya kuma yabawa dubbannin mutanen da suka nuna mubaya'arsu ga sanata Agom, mai wakilar jihar Cross Ribas ta arewa.

"Zan iya cewa tun lokacin tsohon shugaban majalisar dattijai, Joseph Wayas, rabon da mu haɗa dandazon mutane irin wannan a Cross Ribas ta Arewa."
"Hakanan zan iya cewa mazabar Cross Ribas ta arewa bata taɓa samun sanata mai farin jini ba kamar Jarigbe Agom."

Kara karanta wannan

Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a zaben karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna

Ɗan takarar babbar jam'iyyar hamayya PDP, Francis Zimbo, ya lashe zaɓen ƙaramar hukumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna, wanda aka gudanar ranar Asabar.

The Cable ta ruwaito cewa baturen zaɓen karamar hukumar, Nuhu Garba, shine ya sanar da sakamakon zaɓen ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel