Gwamna Tambuwal ya bayyana shirin da Jam’iyyar PDP take yi a game da zaben 2023

Gwamna Tambuwal ya bayyana shirin da Jam’iyyar PDP take yi a game da zaben 2023

  • Aminu Waziri Tambuwal yace jam’iyyar PDP ta fara namijin kokarin karbe mulkin kasar nan a zaben 2023.
  • Gwamnan jihar Sokoto ya bayyana wannan a lokacin da suke zawarcin tsohon gwamna, Olusegun Mimiko.
  • Shugaban gwamnonin na jam’iyyar hamayya ta PDP yace suna sa rai Dr. Mimiko ya sauya-sheka zuwa PDP.

Ondo - Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP na kasa, Aminu Waziri Tambuwal, yace PDP na bakin kokarinta na komawa kan mulki a 2023.

Punch ta rahoto gwamnan na jihar Sokoto yana wannan jawabi a lokacin da ya zanta da manema labarai a gidan tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko.

Da yake jawabi a garin Ondo a ranar 28 ga watan Oktoba, 2021, Aminu Waziri Tambuwal yace jam’iyyar PDP ta dage wajen ganin ta sake rike Najeriya.

Kara karanta wannan

PDP ta yi babban kamu, tsohon Gwamna ya tattara daukacin ‘Yan jam’iyyarsa sun sauya-sheka

Wike, da Ikpeazu sun yi wa Tambuwal rakiya

Rt. Hon. Aminu Tambuwal ya yi wannan bayani ne yana tare da gwamnonin jihohin Oyo, Ribas, da Abia; Seyi Makinde, Nysom Wike, da Okezie Ikpeazu.

Gwamna Tambuwal
Gwamnonin PDP sun yi taro Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

“Za mu canza akalar kasa, mu tabbatar da PDP ta koma kan mulki a 2023.” – Tambuwal.
“Mun zo nan garin Ondo, gidan jagoranmu, Olusegun Mimiko, domin mu sake gayyatar shi zuwa gidan da ya baro, PDP.”
“Kuma kamar yadda ku ke gani, muna tare da gwamnonin Ribas, Oyo da jihar Abia, kuma mun tattauna da shi sosai.”

PDP tana zawarcin Mimiko da yaransa

A jawabinsa, Tambuwal yace suna sa rai su ji alheri ba da dadewa ba, daga bakin tsohon gwamnan, kuma babban jagoran adawa a yankin kudu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ZLP ta ruguje yayin da shugabanta da mambobi suka koma PDP

A cewar gwamnan na Sokoto, sakonsu ga Dr. Mimiko shi ne, ya dawo jam’iyyar PDP ta yadda za a canza akalar mulkin Najeriya a zabe mai zuwa na 2023.

Rahotanni daga Daily Post sun ce ana sa rai Mimiko da sauran ‘yan siyasar su bi jam’iyyar PDP.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnonin sun zauna da Mimiko; tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi; Gboye Adegbenro da wasu ‘yan siyasa.

A jiya aka ji dimbin ‘ya’yan jam’iyyar ZLP sun hallara a gidan Mimiko a garin Ondo domin tarbar tawagar jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Seyi Makinde.

Asali: Legit.ng

Online view pixel