Guguwar sauya sheka: PDP ta yi babban kamu na wani tsohon minista bayan ya bar APC

Guguwar sauya sheka: PDP ta yi babban kamu na wani tsohon minista bayan ya bar APC

  • Tsohon ministan sufuri, Ibrahim Isa Bio ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki zuwa PDP
  • Bio ya sauya sheka ne tare da magoya bayansa a gudunmarsa ya Gure/Gwasoro da ke karamar hukumar Baruten na jihar Kwara
  • Ya samu kyakkyawar tarba daga babbar jam'iyyar adawar kasar wacce ke ganin hakan zai kara mata karfi kasancewarsa gogaggen dan siyasa da ake ganin girmansa a jihar

Jihar Kwara - Tsohon ministan sufuri, Ibrahim Isa Bio ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Tsohon kakakin majalisar na jihar Kwara ya sauya sheka tare da magoya bayansa a gudunmarsa ya Gure/Gwasoro da ke karamar hukumar Baruten na jihar Kwara, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon minista tare da daruruwan mambobin jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa PDP

Guguwar sauya sheka: PDP ta yi babban kamu na wani tsohon minista bayan ya bar APC
Guguwar sauya sheka: PDP ta yi babban kamu na wani tsohon minista bayan ya bar APC Hoto: The Nigeria Voice
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa a Ilorin, sakataren labarai na jam’iyyar a jihar Kwara, Tunde Ashaolu, ya yiwa Bio maraba da zuwa PDP.

Ya kuma yaba masa a kan daukar wannan gagarumin mataki na dawowa jam’iyyar.

Ya ce:

“Matakin ya nuna muradin al’umman Kwara wadanda suka gaji da mulkin kama karya na Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq. Muna yiwa tsohon minista Ibrahim Isa Bio da mabiyansa maraba da zuwa cikin iyalan PDP a Kwara.
“Mun yaba da matakin da ya dauka na yasar da APC da hadewa da jam’iyyarmu da ke kara karfi.”

Ashaolu ya nuna yakinin cewa sauya shekar Bio zai karfafa jam’iyyar kasancewarsa jagora da ake mutuntawa kuma kwararren dan siyasa.

Jaridar Thisday ta kuma rahoto cewa Ashaolu ya ce kofofinsu a bude take ga duk dan siyasar da ya yarda da manufofin jam’iyyar da kuma kawo sabon sauyi a 2023.

Kara karanta wannan

Wani dan majalisa ya koma jam'iyyar PDP ana saura kwana 11 zabe a Anambra

2023: Saraki ya bayyana yadda PDP za ta yi da tikitinta na shugaban kasa

A wani labarin, mun ji cewa gabannin babban zaben 2023, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki, ya yi tsokaci a kan tsarin da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta bi wajen zabar dan takarar shugaban kasa.

Saraki ya ce duk da cewar PDP ta mika tikitin ciyaman dinta na kasa ga yankin arewa ta tsakiya, bata da niyar hana kowani dan takara daga kowani yanki neman shugabancin kasa.

Jaridar Sun ta rahoto cewa Saraki ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Arise TV ta yi da shi ranar Talata, 26 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel