Shugabacin Najeriya a 2023: Jerin kungiyoyi 20 da ke goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa

Shugabacin Najeriya a 2023: Jerin kungiyoyi 20 da ke goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa

Gabanin zabukan shekerar 2023 mai zuwa, kungiyoyi sun ci gaba da nuna goyon baya kan fafutukar neman shugabancin Najeriya na Tinubu.

Kamar yadda jaridar The Nation ya ruwaito, jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba a shekarar 2023.

Sai dai kuma an yi ta gangamin siyasa a wurare daban-daban da ke nuna goyon bayansa na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Shugaba a 2023: Jerin manyan kungiyoyi da suka nuna goyon baya ga Tinubu a zabe mai zuwa
Bola Ahmed Tinubu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, hotunan yakin neman zaben Tinubu, wanda ya kasance tsohon gwamnan Legas sun yi ta bayyana a sassan Najeriya da Birtaniya da kuma Amurka.

Babu shakka, Tinubu zai iya samun goyon baya duba da yawan mabiyansa, kuma masu goyon bayansa a siyasa suna yawa kullum.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar Yarbawa ta tsaida ‘Dan takararta tilo a zaben Shugaban kasa daga APC

Legit.ng ta tattaro cewa ya samu goyon bayan dimbin sarakunan gargajiya a fadin kasar nan, inda wasu daga cikinsu suka ba shi mukamai na karramawa domin nuna jin dadinsu da irin gudunmawar da yake bayarwa a kasar.

A halin da ake ciki dai, akwai kungiyoyin goyon baya na fafutukar ganin Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023.

Binciken jaridar ya nuna cewa sama da kungiyoyin goyon baya 120, musamman a shafukan sada zumunta ne ke tallata burin shugaban kasa na Tinubu.

Ga wasu daga cikin kungiyoyin goyon bayan da aka jero a matsayin wadanda ke zawarcinsa ya gaji Muhammadu Buhari a zaben 2023:

 1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany
 2. Southwest Agenda 2023 group
 3. Tinubu Support Group
 4. Bola Ahmed Tinubu (BAT) 2023
 5. Disciples of Jagaban (DOJ)
 6. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu – B.A.T National Forum
 7. Tinubu for President 2023
 8. Tinubu 2023 Support Group
 9. Tinubu Solidarity Group
 10. Northern Alliance for Tinubu 2023
 11. Bola Ahmed Tinubu Group – USA
 12. Tinubu Transformation Agenda 2023
 13. I Love Tinubu; Tinubu Mandate Group
 14. Asiwaju Ahmed Bola Tinubu Northerners
 15. Tinubu Peoples Network; Vote Tinubu 2023
 16. Tinubu Grassroots Movement
 17. Southwest Agenda 2023 group
 18. Northern Region Supports Tinubu 2023 for President (NRST-23)
 19. The Forum of Political Parties
 20. The Arewa Youth Alliance

Kara karanta wannan

Jerin tafiye-tafiye 9 da shugaba Buhari ya yi zuwa kasashen waje a shekarar 2021

Yayin da wasu ke ganin Bola Tinubu a matsayin jigo kuma wanda APC za ta iya amincewa ta tsayar a 2023, 'yan jam'iyyar adawa ta PDP ba a barsu a baya ba.

A bangaren PDP, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya bayyana cewa, shi ne zai iya gyara Najeriya ta hanyar gogewarsa, inji rahoton The Nation.

Atiku zai iya gyara Najeriya: Gwamna ya bayyana gogewar Atiku da PDP a iya mulki

A bangare guda, yayin da wasu ke goyon bayan Tibunu, Ahmadu Fintiri, gwamnan jihar Adamawa, ya ce zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar baya idan ya sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa, Fintiri wanda shi ne shugaban kwamitin taron gangamin jam’iyyar PDP na kasa ya bayyana haka ne a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a gidan talabijin na Channels TV a shirin Politics Today.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

Gwamnan na jihar Adamawa ya ce Atiku na da dukkan abubuwan da ya kamata na mulkin Najeriya, yana mai jaddada cewa zai yi kokarin ganin ya zama shugaban Najeriya idan ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel