Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a zaben karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna

Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a zaben karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna

  • Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan ta sha kashi a hannun PDP a zaɓen karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna
  • Baturen zaɓe a karamar hukumar, Nuhu Garba, ya sanar da ɗan takarar PDP, Francis Zimbo, a matsayin wanda ya lashe zaɓe
  • Hukumar zaɓe ta jihar ta ɗage zaɓe a wasu kananan hukumomi saboda matsalar tsaro da ta addabe su

Kaduna - Ɗan takarar babbar jam'iyyar hamayya PDP, Francis Zimbo, ya lashe zaɓen ƙaramar hukumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna, wanda aka gudanar ranar Asabar.

The Cable ta ruwaito cewa baturen zaɓen karamar hukumar, Nuhu Garba, shine ya sanar da sakamakon zaɓen ranar Lahadi.

Garba yace Francis Zimbo na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 28,771, wanda ya bashi damar lallasa abokin taƙararsa, John Hassan, na jam'iyyar APC da ya samu ƙuri'u 19,509.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Abokin Atiku Ya Yi Watsi Da Shi, Ya Faɗi Ɗan Takarar Da Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

PDP ta lallasa APC a Kaduna
Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a zaben karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A jawabin baturen zaɓen yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mista Francis Zimbo na jam'iyyar PDP, bayan cike dukan ƙa'idoji da matakan da doka ta tanazar, kuma ya samu mafi rinjayen kuri'u, ina mai bayyana shi a matsayin wanda jama'a suka zaɓa, kuma ya zama zaɓaɓɓe."

Ya sakamakon zaɓen kansiloli?

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa jam'iyya PDP ta lashe kujerun kansiloli 9 daga cikin 11, inda APC ke da guda biyu kacal.

A raanr 4 ga watan Satumba, hukumar zaben jihar ta soke gudanar da zaɓe a wasu ƙananan hukumomi saboda yawaitar matsalar tsaro.

Yaushe aka saka gudanar da zaɓen da aka soke?

A ranar Laraba, Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya bayyana cewa zai naɗa kwamitin riko a kananan hukumomin matukar suka hana a gudanar da zaɓe.

Kara karanta wannan

2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

Aminiya Hausa ta rahoto Gwamnan yace:

"Ina mai tabbatar da cewa matukar zaɓe bai yuwu ba a ranar da aka shirya, to babu wani zaɓi illa mu naɗa shugabanni da zasu tafiyar da kananan hukumomin."
"Saboda haka ya rataya a wuyan kowa dake yankin ku bari a gudanar da zaɓen ko kuma mu naɗa muku waɗanda zasu jagorance ku na tsawon shekaru uku masu zuwa."

A wani labarin kuma Wasu gwamnonin Arewa sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan mutanen da aka kashe a Sokoto

Ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabas ta bada tallafin miliyan N20m ga iyalan waɗanda aka kashe a harin kasuwar Goronyo.

Gwamna Zulum na jihar Borno kuma shugaban ƙungiyar, shine ya kai ziyarar jaje da kuma miƙa tallafin a madadin takwarorinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel