Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo

Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo

  • Jam'iyyar PDP har yanzu bata bayyana yankin da dan takararta a 2023 zai fito ba
  • Amma kawo yanzu, yan siyasan Arewa uku sun bayyana niyyarsu na takara
  • Gwamnan PDP daya tilo a yankin Kudu Maso yamma ya bayyana haka

Lagos - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na da jajirtattun mutane da zasu iya shugabantan kasar nan a 2023.

A cewarsa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal sun bayyana niyyar takara a zaben shugaban kasa mai uwa.

Makinde ya bayyana hakan ne yayin jawabi a hirarsa a tashar ChannelsTV ranar Alhamis.

Gwamnan yace hanya daya tilo da zata ceci jam'iyyar PDP daga barkewa shine gwamnoninta su hada kai da juna gabanin zaben kasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yan jam'iyyar APC akalla 1000 sun kona tsintsiya a jihar Bauchi, sun koma PDP

Yace:

"Hanya daya da zaka iya takawa PDP burki a matakin tarayya shine raba kan 'yayan jam'iyyar."
"Dukkan gwamnonin PDP na sane da haka shiyasa muka amince hada kan juna ya zama abu na farko."
"Yanzu dai jam'iyyarmu PDP na da mutanen da suka cancanci jagorantar kasar nan. Wasu sun bayyana niyyarsu irin mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, kamar gwamna Tambuwal, kamar gwamna Bala Mohammed."

Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo
Atiku, Tambuwal da Kauran Bauchi sun bayyana niyyar takara a zaben 2023, Gwamnan Oyo Hoto: Collage
Asali: Facebook

Yan jam'iyyar APC akalla 1000 sun kona tsintsiya a jihar Bauchi, sun koma PDP

A bangare guda, akalla yan jam'iyyun adawa 1000 a karamar hukumar Dass a jihar Bauchi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) lokaci guda.

Mafi akasarin masu sauya shekan sun fita ne daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bayan zaben shugabannin jam'iyyar ta sake haddasa rikici cikin 'yayan jam'iyyar

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya karyata rade-radin barin jam'iyyar PDP da tsayawa takarar shugaban kasa

Sauran kuma sun fito daga jam'iyyun PRP, NNPP da APGA.

Shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Dass, Alh Sani Korau (Shattiman Dass) ya karbi bakuncinsu a taro na musamman da aka shirya a hedkwatar karamar hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel