Jigon PDP Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi a 2023

Jigon PDP Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi a 2023

  • Jigon jam'iyyar PDP mai adawa a kasar nan, Dr Sampson Orji, ya bayyana cewa Peter Obi ne zabinsa a babban zaben 2023
  • Orji, wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Abiya a inuwar PDP, yace Atiku abokinsa ne amma Obi ya fi shi cancanta
  • Ya sha alwashin yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar tsohon gwamnan Anambra a 2023

Abia - Wani Babban jigon jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Abiya, Dr Sampson Orji, yace ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi, ne zaɓinsa a 2023, ya jingine Atiku.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Orji na ɗaya daga cikin yan takarar sahun gaba da suka nemi tikitin takarar gwamnan jihar Abiya a jam'iyyar PDP.

Mista Peter Obi.
Jigon PDP Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Ayyana Goyon Bayansa Ga Peter Obi a 2023 Hoto: Mr. Peter Obi/facebook
Asali: Facebook

Jigon yace kwarewa da gogewar Peter Obi ta sanya shi ya fita daban a saman sauran masu neman zama shugaban ƙasa, bisa haka ya yanke mara masa baya a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Kara Kaɗa Hanjin PDP Kan Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Mista Orji, tsohon ɗan majalisar ya yi wannan furuci ne a wani shirin gidan Radiyo "Open Parliament”, a Umuahia, babban birnin jihar Abiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma sha alwashin aiki tukuru da tattara wa Obi nutanen da zasu mara masa baya, ba don tsohon gwamnan ya kasance ƙabilarsu ɗaya ba sai don gogewar da yake da ita.

Tsakanin Atiki da Obi, wa yafi cancanta?

Orji ya ƙara da cewa a nemi ya zaɓi ɗaya tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi, tamkar an tambaye shi ya zaɓa tsakanin duhu ne da haske, inda ya ƙara da cewa Obi tamkar wani haske ne.

"Ni ɗan PDP ne har gobe amma zan goyi bayan Peter Obi ba wai don ya kasance Ibo ba saboda abinda yake wakilta. Obi wata tafiya ce, iyalai da abokan arziki na zasu dangwala wa Obi. Atiku abokina ne amma Obi ya fi cancanta."

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Kasa a APC Ya Jingine Tinubu, Ya Faɗi Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

- Dr Sampson Orji.

Bugu da ƙari, bayan kwarewa, daidaito da suka ɗaga Obi, yankin kudu maso gabas ne kaɗai daga kudancin Najeriya ya kamata ya karbi mulkin kasar nan, inji shi.

A wani labarin kuma Jigon APC yace har yanzun suna ci gaba da zawarcin gwamnan Ribas Nyesom Wike

Har yanzu jam'iyyar APC na ci gaba da zawarcin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas domin ya mara wa yan takararta baya.

Jigon jam'iyya mai mulki, Farouk Aliyu, yace Wike mutum ne mai matukar amfani ga kasar nan kuma gwamna mai ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel