Wasu gwamnonin Arewa sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan mutanen da aka kashe a Sokoto

Wasu gwamnonin Arewa sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan mutanen da aka kashe a Sokoto

  • Ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabas ta bada tallafin miliyan N20m ga iyalan waɗanda aka kashe a harin kasuwar Goronyo
  • Gwamna Zulum na jihar Borno kuma shugaban ƙungiyar, shine ya kai ziyarar jaje da kuma miƙa tallafin a madadin takwarorinsa
  • Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, ya nuna jin daɗinsa, tare da kira ga gwamnatin tarayya ta faɗaɗa aikin soji a jihar

Sokoto - Gwamnonin arewa maso gabas ƙarƙashin ƙungiyarsu, sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan waɗanda harin kasuwar Goronyi ya shafa a Sokoto.

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa a ranar 17 ga watan Oktoba, wasu miyagun yan bindiga suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi a Kasuwar Goronyo, mutane da dama suka mutu.

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da gwamna Zulum ya yi a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook.

Read also

Muna neman gwamnatin tarayya ta dawo da hanyoyin sadarwa a jihar Sokoto, Tambuwal

Tambuwal da Zulum
Wasu gwamnonin Arewa sun bada tallafin miliyan N20m ga iyalan mutanen da aka kashe a Sokoto Hoto: The Governor of Borno state
Source: Facebook

Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa ta gabas, Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno, wanda ya bada tallafin a madadin takwarorinsa, ya nuna damuwarsa kan harin.

Yankin arewa yana cikin matsalar tsaro - Zulum

A jawabin da gwamna Zulum ya yi, yace:

"Yankin mu, musamman jihata yana fama da ƙalubalen tsaro da dama wanda suke da alaƙa matsalar mayaƙan Boko Haram."
"Saboda haka zamu cigaba da tallafawa jihar Sokoto sauran jihohin mu na arewa ta yamma dake fama da matsalar yan bindiga da sauran ayyukan ta'addanci."
"Muna fatan Allah ya dawo da zaman Lafiya a Sokoto, kuma a shirye muke domin taimakawa da shawarwari."

Gwamna Zulum, tare da rakiyar Gwamna Muhammad Yahaya na jihar Gombe sun jajantawa gwamnatin Sokoto da kuma al'ummar jihar bisa faruwar wannan lamari.

Read also

Barkewar cutar kwalara: Sama da mutum 500 sun mutu, wasu fiye da 20,000 sun kamu a Jigawa

Me ya kamata gwamnatin tarayya ta yi?

Da yake maratani, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya yaba wa kungiyar gwamnonin arewa maso gabas bisa nuna halin dattako da tausayi.

"Ya kamata gwamnatin tarayya ta faɗaɗa yaƙin da take da yan bindiga zuwa sauran jihohi a yankin arewa maso yamma, domin magance lamarin baki ɗaya."
"Hakanan ya dace FG ta samar da kayan yaƙi ga jami'an tsaro domin su fuskanci yan bindiga yadda ya kamata."

A wani labarin kuma kun ji cewa wasu miyagun Yan bindiga sun fasa gidan yari a jihar Oyo, Sun saki fursunoni baki ɗaya

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin gidan yarin, sannan suka saki dukkan fursunonin dake ciki.

Miyagun yan bindigan sun fasa gidan yari ne da tsakar dare, inda suka yi amfani da gurneti wajen tilasta samun damar shiga harabar gidan gyaran halin.

Source: Legit

Online view pixel