Gwamna ya caccaki ministan shugaba Buhari, Yace ba zai iya lashe zabe a gundumarsa ba

Gwamna ya caccaki ministan shugaba Buhari, Yace ba zai iya lashe zabe a gundumarsa ba

  • Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya soki ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed
  • Gwamnan ya bayyana cewa a halin yanzu ministan ba shi da kataɓus a harkar siyasa, domin ba zai iya cin zaɓe a gundumarsa ba
  • An jima ba'a ga maciji tsakanin Lai Muhammed da gwamnan jiharsa, inda takai ga gudanar da zaɓen shugaban APC guda biyu

Kwara - Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, yace ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, ba zai iya komai ba a siyasance.

Gwamnan ya bayyana cewa ministan ya fi kwari a wajen ɓaɓatu da surutu a kafafen sada zumunta da kuma na watsa labarai.

The Cable ta rahoto Abdulrazaq, yace tsaginsa na jam'iyyar APC shike da yan majalisun dokokin jihar baki ɗaya, banda mutum ɗaya wanda yake tare da ministan.

Read also

Nasarar jam'iyyar PDP na hannun yan Najeriya a zaɓen 2023, Inji Atiku

Gwamnan Kwara da Lai
Gwamna ya caccaki ministan shugaba Buhari, Yace ba zai iya lashe zabe a gundumarsa ba Hoto: fidelinfo.com
Source: UGC

This Day ta rahoto Gwamnan yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Suna ta surutu a kafafen sada zumunta, Lai ba zai iya cin zaɓe a gundumarsa ba, ya fi kwarewa a zuba surutu a kafafen sada zumunta."
"Amma ba su san wahalar da muka ci ba wajen tsaida mambobin majalisar dokoki da kuma ta yadda muka yi muka samu nasarar zaɓe."

Bamu yin siyasar uban gida - Abdulrazaq

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa kowa na iya kokarinsa ne a siyasa babu maganar siyasar uban gida a jihar Kwara.

"Kowane ɗan takara na kokarinsa ne ya samu nasara, amma sai wasu mutane su zauna wuri ɗaya, su bugi kirji suna cewa jam'iyyarsu ce."
"Sun ce bani da kowa a tattare da ni, to su fito su faɗa mana yan majalisa nawa garesu a matakin jiha da na ƙasa? ina da baki ɗaya yan majalisu a tare da ni."

Read also

Bikin sauya sheka: Gwamna ya gana da Buhari, ana zargin zai sauya sheka, ya fito ya yi bayani

"Kwanakin bayan Lai ya zo nan domin ya yi surutunsa, yace shine ya samar da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe, shi ya yi kaza da kaza. Ya yi maganganu da dama kuma ya kai shi har NTA."

A wani labarin kuma Sabbin bayanai kan shirin tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, na sauya sheka zuwa APC

Rahotanni sun bayyana wasu dalilai da yasa har zuwa yanzun tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, bai koma APC ba gabanin 2023.

Majiya mai ƙarfi ta shaidawa Leadership cewa Kwankwaso na fatan tsira da mutuncinsa kuma ya kafa wa APC wasu sharuɗɗa na shiga jam'iyyar.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel