Bikin sauya sheka: Gwamna ya gana da Buhari, ya magantu kan batun komawa APC

Bikin sauya sheka: Gwamna ya gana da Buhari, ya magantu kan batun komawa APC

  • Gwamna Godwin Obaseki ya gana da shugaba Buhari, inda yake jita-jitar zai koma jam'iyyar APC
  • Gwamnan Obaseki ya fito ya yi bayani, inda ya bayyana korarsa aka yi a APC, don haka ba zai dawo ba
  • A cewarsa, PDP ta rufa masa asiri, don haka ba zai yi kuskuren koma jam'iyyar APC ba a yanzu

Abuja - The Nation ta ruwaito cewa, Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya ce mutuncinsa ba zai bari ya iya ficewa daga jam’iyyar PDP ba, jam'iyyar da ta ba shi rufin asiri lokacin da yake cikin bukata.

Gwamna Obaseki ya bada wannan tabbacin ne lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Bikin sauya sheka: Gwamna ya gana da Buhari, ana zargin zai sauya sheka, ya fito ya yi bayani
Gwamnan Edo ya gana da Shugaba Buhari | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Gwamnan, wanda ke mayar da martani kan tsokaci game da yiwuwar komawarsa jam'iyyar APC, ya bayyana cewa bai fice daga jam'iyyar mai mulki ba bisa son ransa, an tilasta masa fita ne.

Kara karanta wannan

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Ya ce da ba zai koma matsayinsa na Gwamna ba ba dan PDP ta taimake shi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake watsi da jita-jitar yiwuwar ficewarsa daga PDP ya koma APC, Gwamnan ya ce:

“Ina ganin na nuna cewa ni dan siyasa ne mai mutunci kuma na bayyana a sarari cewa ban bar daya jam'iyyar ba a kashin kaina, an kore ni daga jam'iyyar ne, wani kuma ya ba ni rufin asiri, ya ba ni dama.
"Ba zai zama abin da ya dace ba a yanzu ka bar wanda ya taimake ka, wanda ya ba ka laima a lokacin ruwa, sannan ka koma ga wanda ya fitar da kai."

Da yake mayar da martani kan rikicin cikin gida da ke ci gaba da wanzuwa a cikin jam’iyyar PDP reshen Edo, gwamnan ya ce a matsayin jam’iyyar da ta sha adawa na tsawon shekaru 12, zai dauki lokaci kafin a samu fahimtar juna tsakanin sabbin mambobi da tsofaffi.

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Mataimakin gwamnan jihar Anambra ya sauya sheka zuwa APC, ya gana da Buhari

Mataimakin gwamnan jihar Anambra, Nkem Okeke, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, ya karbi bakuncin Shugaban kwamitin riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, mataimakin gwamnan Anambra, Dr. Nkem Okeke da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

Mataimakin shugaban kasa a shafukan sadarwa ta zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana labarin sauya shekar tasa a wata sanarwa a Facebook.

Duk da komawa APC, da alamu Fani-Kayode zai fuskanci fushin kotu saboda badakala

A baya kadan, Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Legas ta umarci tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da ya biya tarar N200,000 saboda rashin halartarsa a sake gurfanar da shi da aka yi ko kuma ya fuskanci soke belinsa.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa

Gidan talabijin na Channels ya rahoto cewa, mai shari’a Daniel Osaigor ya ba da umurnin ne a ranar Laraba, yana mai cewa bayan ya duba fayil din kotun, ya lura da wasiku daban-daban guda biyar da ke neman a dage zaman a kan dalilan rashin lafiya.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Fani-Kayode tare da tsohon karamin ministan kudi, Nenandi Usman, da wani Danjuma Yusuf, tsohon shugaban ALGON, da wani kamfani, Jointrust Dimensions Nigeria Limited a gaban kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel