Sabbin bayanai kan shirin tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, na sauya sheka zuwa APC

Sabbin bayanai kan shirin tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, na sauya sheka zuwa APC

  • Wasu sabbin rahotanni sun fito game da shirin tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso na komawa APC
  • Wasu majiyoyi masu ƙarfi sun bayyana cewa Kwankwaso ya kafa wa wakilan APC wasu sharuɗɗa kafin ya koma jam'iyyar
  • Tun bayan kammala wa'adin mulkin Kwankwaso da Ganduje a 2015, har yanzu tsofaffin abokan biyu basa shiri da juna

Kano - Rahotanni sun bayyana wasu dalilai da yasa har zuwa yanzun tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso, bai koma APC ba gabanin 2023.

Majiya mai ƙarfi ta shaidawa Leadership cewa Kwankwaso na fatan tsira da mutuncinsa kuma ya kafa wa APC wasu sharuɗɗa na shiga jam'iyyar.

Kasancewar ana ta cece-kuce kuma shugabannin Arewa na ganin ya kamata a baiwa kudu takarar shugaban ƙasa a 2023, Kwankwaso ya kafawa APC sharaɗin cewa za'a ba shi kujerar mataimaki a 2023.

Kara karanta wannan

Yar majalisar dattijai ta fice daga PDP ta koma jam'iyyar APC, Ta bayyana dalilai

Rabi'u Musa Kwankwaso
Sabbin bayanai kan shirin tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso, na sauya sheka zuwa APC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hakanan kuma Kwankwaso ya shaidawa APC cewa ba za'a yi karambanin ruguza tafiyarsa ta Kwankwasiyya ba a faɗin Najeriya.

Ko ya zata kaya idan Kwankwaso ya koma APC a Kano?

Bugu da kari, Kwankwaso ya bukaci a miƙa masa ragamar jagorancin APC a Kano, maimakon gwamna Ganduje, wanda ya kasance mataimakinsa a baya.

Legit.ng Hausa ta gano cewa ba'a ga maciji tsakanin Kwankwaso da Ganduje tun bayan ƙarewar wa'adin mulkinsu tare a shekarar 2015.

Kwankwaso yana cikin gwamnonin Arewa da suka balle daga PDP a shekarar 2014, daga baya suka shiga APC kuma ta samu nasarar lallasa PDP a zaɓen 2015.

Masana na ganin tsohon abokin Kwankwaso, mataimakinsa kuma gwamnan Kano na yanzu, Ganduje, ba zai amince ya miƙa jagorancin APC a jihar ba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hukumar EFCC ta yiwa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso tambayoyi

Shin APC ta amince da sharuɗɗan Kwankwaso?

Wata majiyar ta daban kuma ta bayyana cewa jam'iyyar APC ba ta amince da bukatun Kwankwaso ba, amma ta ba shi damar shigowa ya nemi abinda yake so.

"Mutanen dake tattaunawa kan dawowarsa a madadin jam'iyya sun faɗa wa Kwankwaso cewa, yana da cikakkiyar damar shiga APC, kuma ya nemi duk kujerar da yake so, amma ba za'a ɗauki bukatunsa a matsayin yarjejeniya ba."
"Hakanan kuma an tabbayar masa da cewa, babu tabbacin za'a bashi mataimakin shugaban ƙasa a 2023 da kuma jagorancin APC, amma zai iya cika burikansa da kan shi."

Kwankwaso ya masanta wannan rahoto a baya

A watan Yuni, Kwankwaso ya musanta rahoton ficewa daga jam'iyyar PDP, tare da komawa APC mai mulki.

Mai taimakawa Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ya bayyana cewa rahoton dake yawo kan shirin Kwankwaso na komawa APC ƙarya ce zalla.

Gwamnatin Kano ta yi martani

Yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC, ranar Alhamis, kwamishinan raya karkara, Musa Iliyasu Kwankwaso, yace suna maraba da dawowar Kwankwaso APC.

Kara karanta wannan

Zargin batanci: Rikici ya barke tsakanin Sheikh AbdulJabbar Kabara da Lauyoyinsa a Zaman Kotu

Musa, wanda ɗan uwa ne ga Kwankwaso, ya bayyana cewa har yanzun ba su cire tsammanin ganin tsohon gwamnan a APC ba, amma bai bayyan lokacin dawowarsa ba.

"Idan ya amince ya zauna ƙarƙashin jagorancin gwamna Ganduje, to muna maraba da shi, Ganduje shine jagoran APC a Kano."

A wani labarin kuma Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Vandeikya, jihar Benuwai.

Dailytrust ta rahoto sanata mai wakiltar Benuwai ta kudu, Abba Moro, na cewa jam'iyyarsa ta PDP ce kaɗai zata iya magance matsalolin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel