Nasarar jam'iyyar PDP na hannun yan Najeriya a zaɓen 2023, Inji Atiku

Nasarar jam'iyyar PDP na hannun yan Najeriya a zaɓen 2023, Inji Atiku

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar yace yan Najeriya dun gaji da mulkin APC kuma sun fara shirin dawo da PDP
  • Atiku yace a halin yanzu mutane basu da wani zaɓi da ya wuce su sake amincewa da PDP a babban zaɓen 2023
  • A ranar Asabar ne, PDP ta gudanar da gangamin tarukanta a matakin jihohi domin zaɓen shugabanninta

Adamawa - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana yaƙininsa cewa yan Najeriya zasu sake miƙa ragamar mulkin Najeriya ga jam'iyyar PDP a 2023.

Atiku ya roƙi yan siyasa su girmama dokokin zaɓen jam'iyya da kuma kundin tsarin mulkin ƙasa yayin gudanar da kowane irin zaɓe.

Punch ta rahoto tsohon mataimakin shugaban yana cewa matuƙar ana son ɗorewar demokaraɗiyya to sai an tabbatar da ingancin zaɓe.

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Dokpesi

Atiku Abubakar
Yan Najeriya basu da wani zaɓi da ya wuce jam'iyyar PDP a zaben 2023, inji Atiku Hoto: Atiku Abubakar FB Fage
Asali: Facebook

Atiku ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan ya kaɗa kuri'arsa a wurin taron zaɓen shugabannin PDP a matakin jiha.

Yace:

"Idan kuka diba zaku ga yadda zaben ke tafiya cikin adalci kuma ba ɓoye-ɓoye A lokuta da dama muna zama ne mu amincewa juna a kowane mataki."

Sama da wakilai 2,000 ne suka kaɗa kuri'a a Adamawa

Rahoto ya nuna cewa sama da wakilan PDP 2,614 daga ƙananan hukumomi 21 na jihar Adamawa ne suka kaɗa kuri'arsu a wurin zaɓen.

Gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, shima ya samu damar zuwa ya kaɗa kuri'arsa a wurin babban taron jam'iyyarsa ta PDP.

Kwamitin tantancewa na jam'iyyar PDP a jihar Adamawa, ƙarƙashin jagorancin Mamu Alhaji Mohammed, ya tantance yan takara 39 dake neman muƙamai daban-daban.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar

A wani labarin kuma kun ji cewa Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a jihar Oyo

A sanarwar da ta fitar ranar Asabar da safe, APC tace ya zama wajibi ta ɗauki wannan matakin saboda wasu bayanai da ta gano.

Tuni dai shugaban kwamitin riƙo, gwamna Mai Mala Buni, ya umarci kwamitin da aka tura jihar ya dawo Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel