2023: Babu dan takarar shugaban kasa da ya zarce Tinubu nagarta, Inji Ganduje

2023: Babu dan takarar shugaban kasa da ya zarce Tinubu nagarta, Inji Ganduje

  • Dakta Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano, ya ce yan arewa ba su da wani zabi da ya wuce su goyi bayan Tinubu ya gaji Buhari
  • Ganduje ya ce jagoran APC na ƙasa ya yi ruwa ya yi tsaki har Buhari ya samu nasara a 2015, dan haka lokaci ya yi za'a saka masa
  • Shugaban ƙungiyar matasan arewa magoya bayan Tinubu (NYTP) yace kaunar cigaban Najeriya da Tinubu ke yi ya sa suke kaunar shi

Kano - Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, yace mutanen yankin arewacin Najeriya ba su da ɗan takarar da zasu goyi baya wanda ya zarce Bola Tinubu.

Punch ta rahoto cewa Ganduje ya yi wannan furucin ne a a wurin bikin kaddamar da kungiya magoya bayan Tinubu 'Northern Youth Professionals for Tinubu' wanda ya gudana a hanyar Haɗeja, Kano, ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Bama-baman' da yan bindiga suka ɗana sun tashi da rayukan dandazon Mutane a jihar Neja

Gwamnan, wanda daraktan hukumar kula da ababen hawa ta jihar Kano, Dakta Baffa Babba Dan’agundi, ya wakilta, yace ya zama wajibi yan arewa su maida bikin da mutane kudu ta yamma suka musu a 2015.

Gwamnan Kano. Dakta Abdullahi Umar Ganduje
2023: Babu dan takarar shugaban kasa da ya zarce Tinubu nagarta, Inji Ganduje Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yace al'ummar yankin da jagoran APC na ƙasa ya fito, Kudu maso yamma, sun goyi bayan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, dan haka lokaci ya yi arewa zata saka musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, mutanen arewacin Najeriya, babu wani ɗan takara da zasu zaɓa a zaɓen 2023 dake tafe sai Bola Tinubu.

A rahoton Vanguard Ya ce:

"Arewacin Najeriya ba su da wani zaɓi sai goyon bayan ɗan takarar Yarbawa kuma Tinubu. Idan na tambaye ku, ku faɗa mun mutumin ya goyi bayan Buhari 100 bisa 100 na san Tinubu ne amsar."
"Lokaci ya yi zamu tabbatar da cewa mu 'ya'yan halas ne iyayen mu suka haife mu. Lokaci ya yi kuma muna tare da takarar Bola Tinubu."

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Rikici ya barke a mahaifar shugaba Buhari Daura kan wanda za'a ba takara a APC

"Mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na ɗaya daga cikin masu goyon bayan wannan tafiya, don haka muna bayan Tinubu a 2023."

Meyasa kungiyar NYTP ta zabi goyon bayan Tinubu?

A nasa jawabin shugaban ƙungiyar NYTP, Abdullahi Tanko Yakasai, ya ce dalilin da yasa suka zabi goyon bayan Tinubu shi ne sabida yana kaunar cigaban Najeriya.

Ya yi bayanin cewa Tinubu ɗan Najeriya ne na gani na faɗa, idan har ya samu damar darewa mulki, zai magance matsalar tsaro kuma ya saita tattalin arzikin ƙasa.

A wani labarin na daban kuma Awanni bayan dagewa, jam'iyyar APC ta sake sanya ranar babban gangamin taronta na kasa

Bayan ɗage taron a dazu, kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa ya zaɓi ranar 26 ga watan Maris, 2022 a matsayin ranar babban taron APC na ƙasa.

Sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe, shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Hedkwatar APC ta ƙasa dake Abuja.

Kara karanta wannan

Abokai sun lakadawa mutumi dukan tsiya har ya mutu kan batan waya, aka ga wayar kasan Kujera

Asali: Legit.ng

Online view pixel