Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta sake sanya ranar babban gangami na kasa a watan Maris

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta sake sanya ranar babban gangami na kasa a watan Maris

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta zaɓi ranar 26 ga watan Maris a matsayin ranar babban gangamin taronta na ƙasa
  • Sakataren APC na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce za'a fara ayyukan babban taron tun ranar 24 ga watan Fabrairu
  • Ya kuma bayyana jadawalin zabukan shugabanni APC na shiyyoyi har zuwa zaben shugabanni na ƙasa

Abuja - Bayan ɗage taron a dazu, kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC ta ƙasa ta zaɓi ranar 26 ga watan Maris, 2022 a matsayin ranar babban taron APC na ƙasa.

Tun da farko jaridar Daily Trust ta rahoto cewa babban taron wanda jam'iyyar ta shirya gudanarwa ranar 26 ga watan Fabrairu, ta ɗage shi har sai baba ta gani.

Sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe, shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Hedkwatar APC ta ƙasa dake Abuja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC mai mulki ta ɗage gangamin taron ƙasa, ta sa ranar taron shiyyoyi

Jam'iyyar APC
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta sake sanya ranar babban gangami na kasa a watan Maris Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Jim kaɗan bayan fitowa daga taron sirri, wanda ya shafe awanni da dama, Sakataren ya ce za'a fara shirye-shiryen taron a ranar 24 ga watan Fabrairu, 2022.

Ya kara da bayanin cewa APC zata gudanar da tarukan shiyyoyi kafin ranar babban taro na ƙasa da ta sanya 26 ga watan Maris.

The Cable ta rahoto Sakataren APC ya ce:

"Bayan tattaunawa da amincewa, kwamitin rikon kwarya CECPC mun amince da fara ayyukan babban taro na ƙasa ranar 24 ga watan Fabrairu, a karkare da a filin Eagle Square ranar 26 ga watan Maris."
"A tsakanin wannan lokacin, mun kuma amince da gudanar da tarukan shiyyoyi a faɗin kasa."

Jadawalin zaben shugabannin shiyyoyi

1. Ranar Alhamis 24 ga watan Fabrairu, 2022, za'a fitar da kwamitocin zaɓen shiyyoyi.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Ana kyautata zaton Buhari zai zauna da gwamnoni domin dinke rikicin APC

2. Ranar Asabar 26 ga watan Fabrairu, 2022, za'a gudanar da taron masu ruwa da tsaki na shiyyoyi.

3. Za'a buɗe damar siyan Fam ɗin ofisoshin shugabannin shiyyoyi daga ranar Litinin 28 ga watan Fabrairu zuwa ranar Alhamis 3 ga watan Maris, 2022.

4. Za'a tantance yan takara a ranar Asabar 5 ga watan Maris, 2022.

5. Za'a sanar da sakamakon tantance yan takara ranar Lahadi 6 ga watan Maris.

6. Ranar Talata 8 ga watan Maris, za'a amince da rahoton tantance yan takara.

7. Za'a gudanar da tarukan shiyyoyi na APC a ranar Asabar 12 ga watan Maris, 2022.

8. Sauraron korafi kan taron shiyyoyi ranar Litinin 14 ga watan Maris, 2022.

9. Amincewa da rahoton ranar Laraba 16 ga watan Maris, 2022.

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje ya bayyana sunan wanda yake goyon bayan ya gaji Buhari a 2023

Dakta Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano, ya ce yan arewa ba su da wani zabi da ya wuce su goyi bayan Tinubu ya gaji Buhari.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shugaba Buhari Ya Baro Brussels Domin Koma Wa Aso Rock

Ganduje ya ce jagoran APC na ƙasa ya yi ruwa ya yi tsaki har Buhari ya samu nasara a 2015, dan haka lokaci ya yi za'a saka masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel