Ana wata ga wata: Rikici ya barke a mahaifar shugaba Buhari Daura kan wanda za'a ba takara a APC

Ana wata ga wata: Rikici ya barke a mahaifar shugaba Buhari Daura kan wanda za'a ba takara a APC

  • Yayin da ake ta shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi a Katsina, rikici ya barke a jam'iyyar APC reshen Daura, mahaifar Buhari
  • Bayanai dake fitowa sun nuna cewa mambobin APC sun banɗare bayan canza sunan wanda ya samu nasara a zaɓe da wani daban
  • Shugaban waɗan da suka ware ya yi kira ga gwamna Masari ya gaggauta shiga lamarin don kada APC ta sha ƙashi a zaɓe

Daura, jihar Katsina - Fusatattun mambobin APC a karamar hukumar Daura, jihar Katsina sun ja daga kan zargin ƙaƙaba musu ɗan takarar kujerar ciyaman.

Garin Daura dake jihar Katsina, nan ne asalin garin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya fito, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Da yake jawabi a madadin mambobin da suka banɗare, shugaban ƙungiyar tsofaffin Kansiloli reshen jihar, Alhaji Ibrahim Suleiman, ya yi zargin murdiya a zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Daura: Shugaban jam'iyya na jihar ya yi fashin baki

Jam'iyyar APC
Ana wata ga wata: Rikici ya barke a mahaifar shugaba Buhari Daura kan wanda za'a ba takara a APC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya yi zargin cewa zaben fidda gwamnin da aka gudanar, wani Alhaji Shehu Abdu, shi aka bayyana ya lashe zaɓen, amma akai masa fin ƙarfi aka maye gurbinsa da Bala Musa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa shi wannan Bala Musa, ɗan uwa ne ga tsohon shugaban hukumar tsaron farin kaya, DSS, Lawal Musa Daura.

Ina wanda ya samu nasarar yake?

Suleiman ya bayyana cewa wanda ya samu nasara a zaɓen yanzu haka yana karkashin bincike, kuma kwamishinan masarautar Daura na da hannu a matsalar da aka jefa mutumin.

Ya ce:

"Ina mai bayyana cewa an jefa Alhaji Shehu Abdu cikin matsala, an laƙaba masa zargin cewa ya karbi kuɗi hannun matasa da sunan zai samar musu aiki."
"Yanzu haka yana tsare a ofishin CID na jihar Katsina, muna tattauna wa da lauyoyin mu kan yadda zamu ɗauki lamarin. Abun takaici haka na faruwa a mahaifar Buhari."

Kara karanta wannan

2023: Matashin ɗan takara dake son gaje kujerar Buhari ya shiga jihar Neja, ya nemi albarkar IBB

"Matsalar na neman zama babbar barazana ga jam'iyya domin alama ce ta hatsari babba yayin da ake fuskantar zaɓen 2023."

Muna kira Masari ya shiga lamarin

Suleiman ya yi kira ga gwamna Aminu Bello Masari ya sa baki a cikin lamarin cikin gaggawa domin gujewa rashin nasarar APC a zaben dake tafe a watan Afrilu.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Bello dake neman takarar shugaban ƙasa a 2023 ya nemi taimakon yan Najeriya kan cimma kudirinsa

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello , ya roki shugabannin APC na jiharsa su fara nuna masa soyayya game da takara a 2023.

Bello, ɗaya daga cikin waɗan da suka ayyana takarar kujerar shugaban ƙasa, yace ya kamata gida su fara nuna masa tsantsar goyon baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel