Dokar Jinsi: Bobrisky zai Nunawa Trump Yadda Aka Mayar da Shi Mace

Dokar Jinsi: Bobrisky zai Nunawa Trump Yadda Aka Mayar da Shi Mace

  • Fitaccen dan daudu Idris Okuneye, watau Bobrisky, ya mayar da martani ga dokar sabon shugaban Amurka, Donald Trump kan jinsi
  • Dan daudun ya bayyana cewa ya tabbata mace ce shi kuma zai gabatar da shaidar da ta tabbatar da hakan idan an bukata
  • Jama’a a kafafen sada zumunta sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan martanin Bobrisky, wasu na ganin wasa yake yi, wasu kuma suka gargade shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan dokar da ke amincewa da nau’in jinsi biyu kawai— namiji da mace— tun ranar farko da ya fara aiki a ofis.

A jawabinsa na rantsuwa, Trump ya tabbatar da wannan mataki, yana mai cewa daga ranar, gwamnatin Amurka za ta amince da jinsi biyu ne kawai a dukkan manufofinta.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Bobrisky
Bobrisky zai bayyana yadda ya zamo mace ga shugaban Amurka. Hoto: @bobriksy222, @donaldtrump
Asali: Instagram

Martani ya biyo baya daga Bobrisky, wanda ya bayyana a shafinsa na Instagram cewa ba ya jin tsoron dokar kuma yana da tabbacin kasancewarsa mace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dokar Donald Trump kan nau’in jinsi

Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya hannu kan dokar da ke tabbatar da jinsi biyu kawai a Amurka, yana mai cewa wannan zai zama doka daga ranar da ya hau mulki.

Rahoton BBC ya nuna cewa shugaba Trump ya ce:

"Za mu tabbatar da cewa dukkan manufofin gwamnati sun danganci jinsi biyu kawai, namiji da mace."

Wannan matakin ya samu goyon baya daga magoya bayan Trump, musamman ma masu kishin kasa.

Tun bayan da Trump ya furta tabbatar da dokar 'yan Najeriya suka fara magana kan shahararren dan daudun da aka fi sani da Bobisky.

Martanin Bobrisky ga dokar Trump

Vanguard ta wallafa cewa Bobrisky, wanda ya kasance daya daga cikin manyan 'yan daudu masu shafe-shafe a Najeriya, ya mayar da martani kan kalaman shugaba Donald Trump na Amurka.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su

Dan daudun ya ce:

“Trump ya ce jinsi biyu ne kawai a Amurka, ko ba haka ba? To ni mace ce yanzu, kuma na dauki matakan da suka tabbatar da hakan.
Idan ana bukatar shaida, zan nuna musu, shikenan.”

A lokacin yakin neman zabe, Trump ya sha nanata cewa zai tabbatar da wannan doka a duk fadin Amurka.

Jama’a sun bayyana ra’ayoyinsu

Jama’a da dama a Najeriya sun nuna martani mabambanta kan kalaman Bobrisky, inda wasu ke ganin wasa yake yi.

Wasu daga cikin masu amfani da kafafen sada zumunta sun shawarci Bobrisky da kada ya yi kokarin daukar matakin da zai kawo masa matsala.

Haka zalika, wasu sun bayyana cewa kalaman Bobrisky wani bangare ne na nishadi kawai, ba tare da wata babbar manufa ba.

Trump ya cire Amurka daga WHO

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya cire kasarsa daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) kan zargin badakala game da cutar Korona.

Kara karanta wannan

"Ban ƙwallafa rai ba": Peter Obi ya canja shawara kan kudurin zama shugaba ƙasa

Shugaba Donald Trump ya zargi hukumar lafiya ta duniya da fifita muradun China da gazawa kan daukar matakan da suka dace a lokacin barkewar cutar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng