Kyakkyawan Matar Aure Ta Saki Bidiyon Mijinta Yana Musu Girki Cikin Nishaɗi A Gida, Tace Ba Zata Koka Ba

Kyakkyawan Matar Aure Ta Saki Bidiyon Mijinta Yana Musu Girki Cikin Nishaɗi A Gida, Tace Ba Zata Koka Ba

  • Bidiyon wata mata da ke nuna mijinta yana musu girki a kicen yana yawo a dandalin sada zumunta
  • A bidiyon, @collierfitfam ta wallafa cewa ta girma ana fada mata cewa mata ne ke girki a kicen
  • Amma, a halin yanzu, mijinta dan Samoan shine ya ke yin kashi 85 cikin 100 na girki a gidan, hakan ya bawa mutane mamaki

Wata mata ta taki sa'a bayan ta auri wani mutum dan kasar Samoa.

Matar, wacce ke amfani da sunan @collierfitfam ta wallafa bidiyon kanta tana rawa a gaban kyamara a yayin da ya ke cewa tun tana yarinya an fada mata mata ke girki a gida.

Miji mai girki.
Kyakkyawan Matar Ta Saki Bidiyon Mijinta Yana Musu Girki Cikin Nishadi A Gida, Tace Ba Zata Koka Ba. Hoto: Image: @collierfitfam/TikTok
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mijina ne ya saba yin girki

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

Bayan wani dan lokaci sai ta kauce daga gaban kyamaran ta nuna 'kakarfan' mijinta ba riga yana girki a kicen.

An kuma hangi mahaifiyarta tana bawa yarinya abinci a yayin da dukkansu suke murmushi.

@collierfitfam ta yi wa bidiyon lakabi da:

"Shi ya ke yin girki kimanin kashi 85 cikin 100. Ba zan iya koka wa."

Bidiyon ya yi farin jini sosai a intanet, inda mata da yawa suke ta yaba wa kakarfan jikin mutumin da kyawunsa.

Kali bidiyon a kasa:

Redneck Barbie ta ce:

"Ina son in ce idan kawai maza yan Samoan masu son aure, ga ni nan."

williamscs7 ta yi tambaya:

"Yana da yan uwa? Kanai, yayyi... ko dangi??."

"Kin yi nasara!!"

Lenagrover ta ce:

"Kawai tana son nuna mana zaddy din ta ne."

Holly Marie ta ce:

"Ina son in mika miki godiya saboda bamu daman ganin wannan mutumin na dan dakika."

Kara karanta wannan

Matashin Miloniya Ya Baje Kolin Hadadden Gidansa da Tsadaddiyar Motar Benz, Bidiyon Ya Yadu

Destiny ta ce:

"Ta yaya ake ji a matsayin daya cikin wadanda ubangiji ke kauna?."

Marol ya tambaya:

"Ina zan iya siyan irin wannan?".

Tiktoker ta ce:

"Mijina yana tambaya me yasa na ke maimaita wannan wakar."

Wani mai baro ya bada mamaki ta yadda ya sauya baronsa ta zama tamkar kanti

Wani matashi mai suna @aramite23 ya bawa mutane sha'awa da mamaki ta yadda ya sauya baronsa ta zama kamar kantin sayar da kayan wayoyi.

A bidiyon, an ga yadda matashin ya cika titi baki daya ba a iya hango fuskarsa ma sai dai kayan wayan.

Mutane sun tsaya suna zuba wa ikon Allah ido domin ba su taba ganin hakan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel