Bidiyon Yadda Wata Matashiyar Mata Ta Hana Mijinta Hutawa a Gida

Bidiyon Yadda Wata Matashiyar Mata Ta Hana Mijinta Hutawa a Gida

  • Wata matar Aure ta hana mijinta shan iska yayin da ta sanya waƙar 'Buga' ta Kiz Daniel da Tekno tana tika rawa a gabansa
  • An hangi matar tana tiƙa rawa mai ban sha'awa da girgiza wa a wani bidiyo da aka wallafa a Soshiyal Midiya
  • Bidiyon ya ja hankalin dubban mutane masu amfani da dandalin TikTok zuwa yanzun sama da mutane 12,000 suka kalla

Wata mai amfani da shafin TikTok ta wallafa bidiyon dake nuna yadda yadda take takura wa abokin rayuwarta yayin da yake zaune dan shan iska.

Maya Kay ce ta wallafa ɗan takaitaccen bidiyon, wanda ya nuna tana rawar wakar Buga a kan cinyoyin mijinta, waƙar da ta haɗa Kiz Daniel da Tekno.

Ba zaman lafiya a Gidan aurenta.
Bidiyon Yadda Wata Matashiyar Mata Ta Hana Mijinta Hutawa a Gida Hoto: @Maya_kay0
Asali: UGC

Mutumin dai na zaune kuma ya maida hankali kan wani abu can daban amma matar ta matsa ya watsar da komai ya koma kanta yayin da ta zo sa salon rawa.

Kara karanta wannan

Duk da Kyauna, “Samarin Shaho” Guduna Suke yi, Budurwa Mai Kamun Kai Tayi Bayani

Matar ta taka rawar Buga a gaban mijinta

Abin sha'awar matashin magidancin ya ƙi nuna fushi wanda a cewar matar dan haka ta kirkiri rawar a gabansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon ya ja hankali ma'abota amfani da dandalin sada zumunta watau TikTok, da yawa sun garzaya rashin faɗar ra'ayoyi sun tofa albarkacin bakinsu.

Kalli bidiyon da matar ta wallafa a nan

Mutane sun maida martani

Queen Vashaty tace:

"Wa ya ga Felicia Osei a nan, gaskiya kun dace da juna."

abenaconstance507 ya ce:

"Ta faɗa masa ya tashi tsaye amma har yanzun yana nan zaune abinsa."

@Bless Kuzagbe558 ta ce:

"Haba 'yar uwa kin matsa da yawa fa."

@Joebel_Klodin ya ce:

"Kalle shi ya wani wayance kamar ba ya jin daɗin abinda take yi."

Wani Magidanci Ya Koka Kan Yadda Matarsa Ke Koransa Daga Gadon Aure Bayan Sun samu ƙaruwa

Kara karanta wannan

Bidiyo: "Ka Biyo Ni Ɗaki Na" Wani Mai Siyar Da 'Ice Cream' Ya Bar Wurin Sana'arsa, Ya Bi Budurwar Da Ta Nemi Ya Ziyarce Ta

A wani labarin kuma Wani Magaidanci Ya Wallafa Bidiyon Halin da matarsa ta jefa shi tun bayan da Allah ya azurta su da samun ƙaruwa

A ɗan gajeren bidiyon an ga matar kwance a kan gado tare da yaron da suka haifa, ta hana mijin ya kwanta don kwasar romon da ya saba a tattare da matarsa.

Ganin haka ya sa ya fara rokon ɗan karamin yaron da ya tausaya masa, lamarin da mutane suka yi ca kan bidiyon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel