"Kantin Tafi Da Gidanka": Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ya Mayar Da Baro Babban Kanti Ya Birge Mutane Sosai

"Kantin Tafi Da Gidanka": Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ya Mayar Da Baro Babban Kanti Ya Birge Mutane Sosai

  • Wani matashin dan Najeriya ya kayyatar da mutane da shagonsa a baro ya cika wuri saboda girma
  • Da ya ke amsa tambayoyi kan yadda ya ke iya tura baron duba da yawan kayan, mutumin ya ce ya gwammace ya yi aiki mai wahala a maimakon sata
  • Yan Najeriya da dama da suka kalli bidiyon yadda ya ke tura baron sun ce yana da kantin tafi da gidanka

Wani bidiyo da @aramite23 ya wallafa ya nuna wani mutumi yana yin wani abu da ba a saba gani ba idan dai ana maganar yawon tallar kayan sayarwa.

A bidiyon, matashin mara lalaci ya cika kayan wayar salula a baro ta yadda ya rufe kusan dukkan sararin da ke tatin.

Dan Najeriya
"Kantin Tafi Da Gidanka": Wani Dan Najeriya Ya Juya Baro Ta Zama Babban Shago, Ya Mamaye Hanya A Bidiyo. Hoto: @aramite23
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Neman kudin da gaske ake yi

Wasu mutane sun tsaya sun kalle shi a yayin da ya wuce su. Idan ana kallon baron daga gaba, ba za a iya ganin fuskar mutumin ba domin kaya sun kare shi.

Kalaman da aka fada kan bidiyon:

"Menene uzurin ka kuma. Neman kudi da gaske."

A wani bidiyo daban, mutumin ya ce yana aiki tukuru ne domin ba ya son yin sata a rayuwarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

A lokacin hada wannan rahoton, kimanin mutane 2000 sun tofa albarkacin bakinsa inda fiye da mutum 100,000 suka latsa 'like'.

Ga wasu cikin tsokacin da mutane suka yi:

Rashgaia ta ce:

"Wannan cikakken shago ne."

oluwafisayomirepe

ya ce:

"Idan ka duba baron sosai, gidan kai kadai ne. akwai ban daki, akwai tukunyar gas, akwai taburma."

majje7595 ya ce:

"Har gidan Iphone 90 yana da shi."

Monny ta ce:

"Wannan shago baki daya ya ke tura wa."

Righteous ya ce:

"Computer Village a baro."

graciousluxliving ya ce:

"Wannan cikakken kanti ne wannan mutumin ya ke da shi."

baby girl ta ce:

"Wannan ta mota za su rika fafatawa kan hanya."

mummy Bee 04

"Ta yaya ya ke ganin hanya. Allah ya saka wa sana'ar ka albarka."

olaideadisa766 ya ce:

"Ta yaya ya ke iya ganin hanya idan tana tura baron. Kamar ya hada baro biyu zuwa uku ne ko kuma amalanke ne?"

Bawan Allah ya makance bayan ya auri makauniya da mijinta ya rabu da ita, sun magantu kan soyayyarsu

Wani mutum mazaunin Tanzania ya bada labarin yadda ya hadu da wata mata makauniya koma sonta ya kama shi har ya aure ta amma daga baya ya makance.

Rashidi Apahamanyi Musasigye, mazaunin garin Arusha a Tanzania yana wurin aikinsa ne lokacin da ya kyalla ido ya hangi, matar Lilian.

Asali: Legit.ng

Online view pixel