Matashin Miloniya Ya Hasko Cikin Katafaren Gidan Da Ya Dankara, Ya Rubuta Sunansa a Harabar Gidan

Matashin Miloniya Ya Hasko Cikin Katafaren Gidan Da Ya Dankara, Ya Rubuta Sunansa a Harabar Gidan

  • Wani matashi dan Najeriya ya burge mutane da dama bayan ya nuna katafaren gidan da ya ginawa kansa
  • Gidan wanda aka yiwa fenti mai kyau da kayan alatu yana dauke da wata hadaddiyar motar Benz pake a wajen ajiye motoci
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon matashin sun ce sun so yadda ya bayar da fifiko wajen ginawa kansa gida

Wani matashi dan Najeriya mai suna @__roddy0, ya je shafin soshiyal midiya domin wallafa bidiyon dankareren gidan da ya ginawa kansa da kuma tsadaddiyar motarsa kirar Mercedes Benz.

Da yake yiwa bidiyon lakabi da "hadadden gidana.", kamarar ya hasko tun daga filin ajiye motoci da ke cikin harabar gidan har zuwa wajen mutanen da tsaya a mashigin ginin.

Matashi da gida
Matashin Miloniya Ya Hasko Cikin Katafaren Gidan Da Ya Dankara, Ya Rubuta Sunansa a Harabar Gidan Hoto: @_roddy0
Asali: UGC

Matashi na more kudinsa a yanar gizo

An yiwa harabar gidan shafe na zamani, yayin da kalar fentin gidan ya dace da kasan. Mutumin ya kuma rubuta sunansa baro-baro a kasan gidan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun yi ta tambayar ko yaushe ni'ima irin wannan zai isa garesu da samun yalwar dukiya irin wannan.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

fundlord ya ce:

"Na tayaka murna dan uwa dan ba zan iya wucewa ba tare da martani ba saboda ina yiwa kaina fatan irin haka."

adepoju337 ya ce:

"Allah sai yaushe."

oluwaskydrick2 ya ce:

"Ubangiji ina bukatar wannan Amin."

Rita Darracott ta ce:

"Ina tayaka murna maigida."

user612491539434 ya tambaya:

"Nawa ka kashe wajen gina gidan nan?"

Shaky Shaky ya amsa:

"Kawai ka ware miliyan 30 dan uwa. zai iya kai maka ya danganta da yadda kake so."

King Pedro ya ce:

"Ya yi kyau dan uwa, ka yiwa kanka kokari sosai."

iamsirlawrence ya ce:

"Ni babu abun da ke yi mun dadi fiye da irin wadannan abubuwan ka samu gida irin wannan sauran duk tarihi ne ina taya ka murna dan uwa."

Matashi ya kashe 1.3 miliyan wajen kera hadadden gidansa

A wani labarin, wani matashi ya yi abun da bahaushe ke kira daidai ruwa daidai tsaki inda ya kera hadadden gidansa irin wanda karfinsa zai iya dauka.

Matashin dai ya kashe naira miliyan 1.3 wajen gina gidansa na jan laka sannan ya yi yabe da siminti kuma abun ya hadu sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel