Saurayi Ya Haɗu Da Sahibarsa Baturiya Bayan Shekara 2 Suna Soyayya A Intanet, Bidiyonsu Ya Sosa Zuciyar Mutane

Saurayi Ya Haɗu Da Sahibarsa Baturiya Bayan Shekara 2 Suna Soyayya A Intanet, Bidiyonsu Ya Sosa Zuciyar Mutane

  • Wata baturiya ta wallafa bidiyon lokacin da a karshe ta hadu da masoyinta bakatar fata bayan shafe shekaru suna soyayya ta intanet
  • A filin tashin jiragen sama na kasar Poland, masoyan biyu sun hadu sun rungumi juna na tsawon dakikai
  • Mutane da dama masu amfani da TikTok wadanda suka ga bidiyon sunyi mamakin yadda soyayyar tasu ta intanet ta dore

Poland - Wani gajeren bidiyo na haduwar wasu masoya biyu bakar fata da farar fata ya dauki hankulan mutane a soshiyal midiya.

A cikin faifan bidiyon, wata baturiya ta tarbi masoyinta bakar fata bayan isowarsa filin tashin jiragen sama na kasar Poland.

Masoya a Poland
A Ƙarshe Saurayi Ya Haɗu Da Sahibarsa Baturiya Bayan Shekara 2 Suna Soyayya A Intanet, Bidiyonsu Ƙayyatar. Hoto: Photo source: TikTok/@blackandwhite.love
Asali: UGC

A karshe soyayya ta yi nasara

Matar a TikTok ta bayyana cewa wannan shine karo na farko da za ta hadu da masoyinta bayan shekaru biyu suna soyayya ta intanet.

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Domin tarbar mutumin, matar ta rike takardar dauke da sunansa a rubuce. Sun rungumi juna a wani yanayi da ke nuna zurfin soyayyar da suke yi wa juna.

Kalli bidiyon a kasa:

A lokacin hada wannan rahoton, a kalla mutane 900 sun tofa albarkacin bakinsa kan bidiyon, yayin da fiye da mutum 19,000 suka yi 'liking'.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin tsokacin da mutane suka yi

Oana9 ta ce:

"Idan har da gaske kuna son juna kuma kuna son zama cikin farin ciki, ku bar wallafin a shafukanku na sada zumunta. Ina muku fatan alheri."

Ines ta ce:

"Soyayya ta shekaru 2 a intanet? wannan ba soyayya bane ko?"

Matar ta bada amsa:

"Wata kila a wurin ka."

Jasmina Andjelkov505maja ta ce:

"Ina taya ku murna daga cikin zuciya ta, yin soyayya ta intanet abu ne mai wahala, amma kun nuna cewa hakan na yiwuwa."

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Biya Kudin Jirgi Daga 'Kasar Waje Dan Ganin Saurayinta

PapaFifi ta ce:

"Garin masoyi ba shi da nisa, ba ruwansa da iyakoki. Ina muku fatan alheri."

Lilian Tarh ta ce:

"Dan uwa, ka kula da matar nan, yar uwa ina kaunan ki, barka da zuwa kasar mu."

Giftkanyoi ta ce:

"Me yasa ni ko mace yar shekara 90 na gaza samu a can."

Brakwame ya ce:

"Yaushe zan hadu da wani a nan."

Baturiya ta taso daga Amurka zuwa Najeriya don auren wani matashi

Wata farar fata yar Amurka mai suna Jaclynn Annette Hunt ta taso tun daga Amurka ta taho Najeriya don haduwa da masoyinta, Bright Cletus Essien.

Ta iso Najeriya ne domin a daura aurensu a garin Obio Ibiono da ke jihar Akwa Ibom a ranar Asabar 17 ga watan Afrilu a wani coci da ke garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel