Daga Magana a Facebook: Baturiya Ta Baro Amurka Don Auren Wani Matashi a Najeriya, Hotunansu Ya Dauki Hankula

Daga Magana a Facebook: Baturiya Ta Baro Amurka Don Auren Wani Matashi a Najeriya, Hotunansu Ya Dauki Hankula

  • Wani dan asalin Jihar Akwa Ibom, Bright Cletus Essien, ya yanke shawarar auren masoyiyarsa wacce Baturiya ce, Jaclynn Annette Hunt
  • Sun hadu da Bright ne a kafar sada zumuntar Facebook kuma ta taho don a yi auren nasu ba tare da ko dan uwanta daya ya biyota ba
  • Nan da nan ‘yan uwa da abokan arzikin angon suka fara wallafawa a Facebook, su na gayyatar mutane auren inda suka ce daga magana a Facebook sai aure

Wata Baturiya ‘yar kasar Amurka, mai suna Jaclynn Annette Hunt ta yi doguwar tafiya don auren masoyinta dan Najeriya, Bright Cletus Essien.

Baturiyar ta taho tun daga kasarta don a yi daurin aurensu a ranar Asabar, 17 ga watan Afirilu, a Cocin Divine Domination Covenant Church of God, Obio Ibiono da ke Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Abin da INEC Take Tsoro Ya Auku, An Sake Kai Wa Ofishin Hukumar Zabe Hari

Daga Fara Magana a Facebook: Baturiya Ta Baro Amurka Don Auren Wani Matashi a Najeriya
Daga Fara Magana a Facebook: Baturiya Ta Baro Amurka Don Auren Wani Matashi a Najeriya. Hoto
Asali: Facebook

Sai dai ba a ga ko mutum daya ba a cikin ‘yan uwan amaryar ba yayin da ‘yan uwa da abokan arzikin angon suka taru wurin shagalin.

Wani abokin angon, Alban Ekandem, yayin da ya yi wallafar a Shafinsa na Facebook ya bayyana cewa masoyan sun hadu ne a kafar sada zumuntar zamani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alban ya ce da farko ya yi tunanin ba gaskiya ba ne, har sai da aka gayyace shi daurin auren. Ya taya abokinsa murna inda ya ce soyayya gaskiya ce.

Kamar yadda ya wallafa:

“Lokacin da aka gayyace ni bikin, ce wa angon na yi shirme ne amma sai ya yi dariya ya ce min za ta zo. Ga ta kuwa ta zo wurinmu yanzu haka.
“Daga fara magana a Facebook kawai sai ta amince da aurensa. Gaskiya Bright ka tabbatar min da cewa soyayya gaskiya ce.

Kara karanta wannan

Ana Yi Wa Rayuwata Barazana Saboda Na Kai Jam’iyyar APC Kotu – ‘Dan Takara

“Jaclynn barka da zuwa Jihar Akwa Ibom da ke Najeriya. Gobe ne za a yi auren. Za mu fara daren angwanci, muna gayyatar ku. Barka dan uwa. Ina matukar taya ka murna.”

Anan ne Alban ya wallafa hotunan auren masoyan. Ga wallafar a kasa:

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel