'Yar jarida Stella ta caccaki Kemi bisa zarginta da kulla soyayya da Fani Kayode a can baya

'Yar jarida Stella ta caccaki Kemi bisa zarginta da kulla soyayya da Fani Kayode a can baya

  • Fitacciyar 'yar jarida ta tono sabon batu kan wani abin da ya faru tsakaninta da wata 'yar jarida akan tsohon ministan sufurin jiragen sama
  • A baya, wata 'yar jarida Kemi Olunloyo ta kakaba zargi kan wata 'yar jarida Stella Dimoko Korkus na kulla soyayya da FFK
  • Sai dai, bata tamka mata ba, sai bayan da kura ta lafa Stella ta dauko batu, kana ta nemi Kemi ta lashe amanta na sharara karya

A wani rahoton GistLover, Fitacciyar 'yar jaridar nan 'yar Najeriya da ke zaune a kasar Jamus, Stella Dimoko Korkus ta yi kira ga Kemi Olunloyo ta nemi lashe amanta kan wani batu, bayan da tsohon minista sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode da matarsa, Precious Chikwendu suka sasanta tsakaninsu.

A 2020, lokacin da Femi Fani Kayode da Precious Chikwendu ke kai ruwa rana game da makomar ‘ya’yansu, Kemi Olunloyo ta zargi Stella Dimoko Korkus da kulla soyayyar wucin gadi da Fani Kayode a shekarun da ya gabata.

Kara karanta wannan

'Zan daɗe ban manta da haɗuwar nan ba' FFK ya shiga shauƙi yayin da tsohuwar matarsa ta ziyarce su shekara 2 da rabuwa

Yadda batu ya fito na zargin karya daga Stella kan Kemi
Sai a fadi gaskiya: Bayan sulhun FFK da matarsa, 'yar jarida ta tono batun sharara karyar Stella na soyayya da FFK | Hoto: gistlover.com
Asali: UGC

Stella, wacce a baya bata taba cewa uffan kan zargin ba, a karshe dai ta magantu bayan da Fani Kayode da Precious suka sasanta rikicin da suke na tsawon shekara biyu.

Tushen lamarin

A cewar rahotanni, Femi Fani Kayode ya kasa boye farin cikinsa da ganin Precious Chikwendu ta ziyarci gidansa a karon farko cikin shekaru biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

FFK ya garzaya shafinsa na Instagram inda ya yi dogon rubutu yana mai murnar dawowarta gidansa.

Tabbas, da muka yi duba ga shafinsa na Instagram, FFK ya yada hoto game da rubutun da ya yi na murnar haka, inda muka ga Precious, yaran biyu da kuma FFK a zaune cikin wani dakin sauke baki.

Martanin Stella

Awanni kadan bayan sulhun, Stella kuwa ta waigo kan Kemi Olunloyo tare da zarginta da sharara karya a kanta a yunkurinta na goyon bayan FFK, inda ta tsaya allan-baran sai dai Kemi ta buga karyar soyayyar domin fadin gaskiya da nuna goyon bayanta ga Precious.

Kara karanta wannan

Kotu ta ki Sauraron Shari'o'in Lauyan da Yayi Shigar Bokaye Zuwa Kotu

A kalamanta kan jita-jitar soyayya da FFK, Stella ta ce su abokai ne ainun amma kowa ya kama gabansa bayan da ya yi amfani da ‘bakinsa mara sakata’ wajen fadawa wata kawarsu marigayiya abubuwan da suka girgiza ta kuma suka ja mata ciwo.

Legit.ng Hausa ta bibiyi rubutun da Stella ta yada a shafinta na Instagram, inda ya dauko asalin rubutun Kemi tare da bayyana kiran.

Kalli rubutun:

Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya

A wani labarin, gogaggiyar jarumar fina-fina ta Nollywood a Najeriya wacce aka dade ana damawa da ita, Eucharia Anunobi, ta ce neman mijin aure ta ke yi cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

A wata tattaunawa da BBC Ibo ta yi da ita, ta ce tana neman namijin da zai sanya mata zoben aure a yatsan ta.

Jarumar mai shekaru 56 ta ce tana fatan samun cikakken namiji, wanda ya ke da duk abinda mace ta ke nema a wurin mijin aure.

Kara karanta wannan

Fitacciyar 'yar fim: Bana zuwa coci, ni musulma ce kuma mai kishin addini na

Asali: Legit.ng

Online view pixel