"Zan daɗe ina ƙaunar wannan lokacin" - FFK yayin da matarsa ta ziyarce su shekara 2 bayan sun rabu

"Zan daɗe ina ƙaunar wannan lokacin" - FFK yayin da matarsa ta ziyarce su shekara 2 bayan sun rabu

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode wato FFK, ya nuna tsantsar farin ciki da ziyarar tsohuwar matarsa har gida
  • Ya ce bayan shekara biyu da rabuwa, Precious Chikwendu, ta ziyarce shi da 'ya'yan su har gida, lokacin ya fi karfin harshe ya bayyana
  • FFK ya yaba wa Precious da wannan ziyara tare da gaya mata cewa kowa a cikin iyalansa da ma'aikata na ƙaunarta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Femi Fani-Kayode ya garzaya shafinsa na Instagram domin zuba kalaman yabo ga tsohuwar matarsa, Precious Chikwendu, yayin da ya gaza rike farin ciki da annashuwar da ya shiga.

FFK ya bayyana yadda ya ji farin cikin ganin tsohuwar matarsa ta sake haɗuwa da shi, iyalansa, da ma'aikatan gidan shi bayan shekaru biyu da rabuwarsu.

Na tsawon watanni, Precious ta zargi FFK da nesanta ta da 'ya'yanta kuma sun jima a gaban Kotu suna tafka mahawara kan wanda zai cigaba da kula da yaran.

Kara karanta wannan

Asirin matar aure ya tonu, Mijinta ya fahimci ta ci amanarsa da mutane 9 a boye

Ziyarar Precious gida FFK.
"Zan daɗe ina ƙaunar wannan lokacin" - FFK yayin da matarsa da ziyarce su shekara 2 bayan sun rabu Hoto: @real_FFK
Asali: Instagram

A wasu yan makonni da suka gabata Presious ta samu damar zuwa ganin 'ya'yanta, ba ta iya rike farin cikin da ta ji ba a lokacin, don haka ta je kai tsaye don gode wa FFk bisa bata damar sake haɗa ido da yaranta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan ne karo na biyu amma ya sha banban da na farko kasancewar Precious ta samu damar shiga har cikin gidan FFK ganin 'ya'yanta ba kamar na farko ba.

Tsohon ministan ya saki Kyawawan Hotuna a Instagram, yana mai kalaman yabo ga tsohuwar matarsa, Precious, da 'ya'yansu daga alaƙar su ta baya.

Kyawawan Kalaman FFK

"Wannan lokaci ne mai tarihi, karo na farko bayan shekara biyu, ko kaɗan bamu yi tsammani ba bayan ta ɗauki 'ya'ayan mu Aragorn, Ragnar, Aiden da Liam zuwa shaƙatawa, Maman Aragorn ta kawo mana ziyara har cikin gida."

Kara karanta wannan

A kan tsohon minista: Mata 'yan jarida biyu na kai ruwa rana akan FFK a shafin Instagram da Twitter

"Shakara biyu Ni da Ita bamu ganin juna ko yi wa juna magana amma da yammacin ranar Asabar mun kwashe abinda bai gaza awanni huɗu ba tare, mun tattauna, mun yi dariya, mun tuna wasu kyawawan lokuta."
"Abun da taɓa rai ganin iyalaina da ma'aikata sun tarbeta hannu biyu, babban ɗan mu Aragorn ya rike hannunta da kyau, ya mata rakiya ta kofar shiga zuwa harabar gida yayin da na zuba musu ido daga sama cikin mamaki."

- FFK

A cewar tsohon ministan sufurin jiragen sama akwai wasu lokuta a rayuwa da kalamai ba zasu iya bayyana farin ciki ba, wannan lokacin na cikin su, inji FFK.

Ya ƙara da cewa bayan tsayin shekara biyu na rashin jituwa ba magana da ɗacin rabuwa, sai ga shi Precious ta ba su kyautar ganinta kuma ta zo har gida.

"Farin ciki da murna ya mamaye ko ina da dawowar wannan babbar zakanya. Kowane ɗaya daga cikin mutane 60 dake rayuwa da aiki a gidan mu ya yi murna da ganinta, wasu sai da suka zubda hawayen farin ciki."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mataimakin gwamna ya maka majalisar dokokin jiha a Kotu kan yunkurin tsige shi

"Zan daɗe ina kaunar wannan lokacin na tsawon shekaru. Wannan babban nasara ce ga duk wasu masoyan zaman lafiya da 'ya'ya maza da mata na gaskiya."

Bayan kalaman jin daɗi marasa adadi, FFK ya kwatanta lokacin da wasu muhimman lokuta na rayuwa tare da gode wa 'Maman Aragorn'. Ya kuma tabbatar mata cewa suna kaunarta a ko da yaushe kuma ba zata gushe ba.

A wani labarin na daban kuma Ambaliyar ruwa ta lakume rayuka, ta lalata gidaje sama da 2,000 a jihar Kano

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya halaka mutum uku da wasu gidaje sama da 2,000 a kananan hukumomi 5 a jihar Kano.

Shugaban hukumar SEMA, Dakta Sale Jili, ya ce tuni hukumar ta kai ɗaukin gaggawa yankunan da abun ya shafa tare da tallafa wa mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel