Kotu ta ki Sauraron Shari'o'in Lauyan da Yayi Shigar Bokaye Zuwa Kotu

Kotu ta ki Sauraron Shari'o'in Lauyan da Yayi Shigar Bokaye Zuwa Kotu

  • Wata baabbar kotun tarayya dake zama a jihar Legas ta ki sauraron shari'o'in dake gabatan wanda lauya Malcolm Omirhobo ya mika
  • Mai Shari'a Tijjani Ringim, ya bukaci lauyan ya kare kansa a rubuce saboda shigar bokaye da yayi ya bayyana a gaban kotu
  • A cewar Omirhobo, tunda kotun koli ta bada damar a yi shiga addini a duk inda aka so, don haka ya koma shigar gargajiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Wata babbar kotun tarayya dake Legas ta ki sauraron kararrakin Malcolm Omirhobo sakamakon bayyana da yayi a gabanta da shigar bokaye.

A ranar Alhamis da ta gabata, Omirhobo yq bayyana a kotun koli sanye da irin kayan. The Cable ta ruwaito.

Lauya Omirhobo
Kotu ta ki Sauraron Shari'o'in Lauyan da Yayi Shigar Bokaye Zuwa Kotu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Lauyan yace yana amfani da damarsa ne sakamakon hukuncin da kotun koli ta yanke wanda ya jaddada cewa dalibai Musulmi suna da damar sanya hijab a makarantu.

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

A ranar Litinin, lauyan mai rajin kare hakkin dan Adam ya bayyana a gaban Mai shari'a Tijjani Ringim, sanye da wadannan kayan na bokaye, lamarin da ya janyo cece-kuce daga lauyoyi wadanda suka musanta cewa ba dole a sauraresa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma Omirhobo yace kundin tsarin mulki ba haka yace ba kuma zai iya zabar yadda zai bayyana a gaban kotu.

"Mai shari'a, babu dokar da ta zarce ta kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya," yace.

Bayan sauraronsa, Ringim ya umarci Omirhobo da yayi bayani ga kotu kan dalilin da zai sa a sauraresa da wannan shia a zaman kotu na gaba.

Kotun ta bukaci bayanin kada ya wuce shafuka biyar tare da ambaton hukumomi inda ya dace, inda ya kara da cewa a gabatar da su kafin ranar da za a shiga kotu na gaba.

Kara karanta wannan

Gwamna da Ministan Buhari sun tono asalin abinda ya haifar da matsalar tsaro a Najeriya

"Ba za ka yi bayani ga kotu a haka ba a matsayin ka na kwararre. Zan dage shari'arku kuma ka zo ka yi bayani ga kotu kan dokar da ta baka damar bayyana a gaban ta kamar haka," Alkalin yace.

Alkalin ya dage sauraron kararrakinsa har biyu zuwa ranar 10 ga watan Oktoban 2022.

Gaskiya Tayi Halinta: Yadda Aka Tirsasa CJN Tanko Yayi Murabus Kan Dole

A wani labar na daban, murabus din alkalan alkalan Najeriya, Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad a ranar Litinin ya biyo bayan wasu manyan fadi-tashi da aka dade ana shiryawa amma aka kaddamar da su a daren Lahadi, majiyoyi da dama da suka san kan lamarin suka tabbatar wa da Daily Trust.

Majiyoyi masu karfi sun ce akasin tunanin da ake na cewa Muhammad yayi murabus da kansa ne, tirsasa shi aka yi daga cikin manyan jami'an tsaro da jami'an gwamnati.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Idan An Kasa Nuna Makarantun da Tinubu ya Halarta, An ga Wadanda Ya Gina

Bayan murabus dinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari'a Olukayode Ariwoola, na biyu a daraja a kotun kolin, a matsayin mukaddashi alkalin alkalan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel