Izala ta musanta kalaman da aka danganta wa Sheikh Kabiru Gombe kan Tinubu, ta ce labarin ƙarya ne, tare da kai ƙorafi ga jami'an tsaro don kama wanda ya yada shi.
Izala ta musanta kalaman da aka danganta wa Sheikh Kabiru Gombe kan Tinubu, ta ce labarin ƙarya ne, tare da kai ƙorafi ga jami'an tsaro don kama wanda ya yada shi.
Sojojin Najeriya sun hallaka babban mai ɗaukar bidiyon Boko Haram, yayin da ƙungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarsa a wani sabon faifan bidiyo da ta fitar.
Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya gwangwaje gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris da sarautar gwarzon daular Usmanuyya saboda taimakon jama'a.
Rahotanni sun tabbatar da tashin gobara a wata makarantar sakandare a jihar Niger inda ake zargin wasu mashaya tabar 'wiwi' da haddasa ta a daren ranar Alhamis.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa za ta ci gaba da aikin da take yi na kai samame kan shagunan caca a jihar. Hisbah ta ce ba za ta sassauta ba.
Yayin da ake shirye-shiryen addu'ar bakwai ta rasuwar mahaifiyar Ahmed Ajobe, ƴan bindiga sun sace ƴan uwan ɗan jaridar a hanyar zuwa kasuwa a Kogi.
Wasu daga cikin 'yan takarar da suka fafata a zaben gwamnan jihar Ondo, sun nuna goyon bayansi ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa. Sun bayyana cewa sun amince da nasararsa.
Gwamnatin tarayya ta bayyana matsayarta kan hana kudade ga jihar Rivers. Ofishin akanta janar na tarayya ya bayyana cewa za a ba jihar kudadenta na watan Oktoba.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta Kano ta taimaki rayuwar wasu daga cikin matasan da aka tuhuma da zargin amanar kasa, inda aka ba su aikin yi a jihar.
Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya yi magana kan liyafar da Sheikh Kabiru Gombe ya halarta inda ya ce kwata-kwata bai dace malamai su halarci irin wannan wuri ba.
Kungiyar kwadago ta ƙasa watau NLC ta ce wa'adin da ta ba gwamnatocin jihohi kan fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi yana nan daram, ta ce ba abin da ya sauya.
Labarai
Samu kari