Rabiu Kwankwaso ya ce Peter Obi zai cika alkawarin yin wa’adin shekaru hudu kacal idan ya lashe zaben 2027, yana mai cewa sun sanya yarjejeniyar a rubuce.
Rabiu Kwankwaso ya ce Peter Obi zai cika alkawarin yin wa’adin shekaru hudu kacal idan ya lashe zaben 2027, yana mai cewa sun sanya yarjejeniyar a rubuce.
Gwamnatin Tarayya ta karyata jita-jitar cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), zai yi murabus, tana mai cewa labarin kirkirarre ne.
Omoyele Sowore ya sanar da cewa ‘yan sanda sun cafke Dele Farotimi bisa zargin ɓata sunan Tony Elumelu. Sowore ya yi kira da a saki lauyan nan take don adalci.
Bayan tantance shi a makon da ya gabata, majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oƙuyede a matsayin hafsan sojojin kasa.
Matasa daga jihohin Arewa 19 sun gudanar da gangami don goyon bayan Sanata Barau Jibrin bisa rawar da yake takawa kan dokokin gyaran haraji da Tinubu ya gabatar.
Gwamnatin Kano ta na zuba ido don a fara sayen kujerun aikin hajjin bana. Hukumar jin dadin alhazai ta koka kan karancin sayen kujerun, yayin da shiri ke kankama.
Majalisar wakilai ta ƙasa ta buƙaci shugaban ƙasa ya tilastawa ministan kudi, Wale Edun buɗe asusun hukumar kula da harkokin walwalar al'umma watau NSIPA.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa an yi arangama tsakanin yan bindiga kan neman iko tun bayan mutuwar Halilu Sububu inda aka kashe wani kwamanda.
An cafke wani mutum mai suna Soja da yake taimakon yan bindiga suna waya domin karbar kudin fansa. Yana ba yan bindiga suna kiran mutane domin a ba su kudi
Majalisar wakilai ta umarci CBN da ta dakatar da sallamar ma’aikata 1,000 da biyan kudin sallama na N50bn, inda ta kafa kwamitin bincike kan lamarin.
NLC ta caccaki kalaman gwamnan Ebonyi. Francis Nwifuru ya yi barazanar korar ma'aikata. NLC ta ce duk ma'aikata da da 'yancin yajin aiki a kan damuwarsu ga gwamnati.
Labarai
Samu kari