Iyalan Mary Habila sun bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sanda ya sa a ba su gawar diyarsu domin jana'iza, sun ki amincewa da gwajin gawa saboda dalilan addini da al'ada.
Iyalan Mary Habila sun bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sanda ya sa a ba su gawar diyarsu domin jana'iza, sun ki amincewa da gwajin gawa saboda dalilan addini da al'ada.
Majalisar dattawa ta kasa ta amince a hana mutane talla da yin wa'azi a cikin motocin haya a Najeriya. Za a rika cin tarar duk wanda ya yi haka N50,000.
Gwamnatin tarayya ta sauya sunan Jami’ar Abuja zuwa Jami’ar Yakubu Gowon don girmama tsohon shugaban kasa. Kudurin yana jiran amincewar majalisar tarayya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ba shi da alaƙa da wani shafin yanar gizo da ake yaɗawa cewa shi ne zai ba da tallafin N65,000.
Kasuwar fetur daga matatar Dangote ta na kara bunkasa. Mataimakin shugaban sashen man fetur da gas na Dangote, Devakumar Edwin ya tabbatar da haka.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC). Tinubu na jagorantar taron ne wanda ake tunanin shi ne na karshe a 2024.
Hafsan sojojin kasa (COAS), Laftanar Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede, ya bayyana cewa sojoji na zafafa kai hare-hare kan 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa.
Babban hafsan tsaron ƙasa, CDS Janar Chirstopher Musa ya ba da umarnin yin bincike don gano gaskiya kan zargin mutuwar shugabannin Okuama a hannun sojoji.
Kotun koli a ranar Litinin, 16 ga watan Disamba 2024, ta yi watsi da karar Ambrose Owuru na neman tsige Bola Ahmed Tinubu daga kujerar shugaban Najeriya.
Gwamnonin Najeriya sun shawarci hukumomi a kan yawan hadurra. Wannan na zuwa bayan mutuwar mutane 20 a Binuwai. Gwamnonin sun kara da mika ta'aziyya ga gwamnati.
Gwamnonin Najeriya 32 sun shirya kashe Naira tiriliyan 22 a shekarar 2025 mai zuwa. A cikin kasafin da suka gabatar, gwamnonin sun yi bayanin yadda za a kashe kudin.
Labarai
Samu kari