Rundunar 'yan sandan Kano ta tabbatar da cewa mutanen karamar hukumar Bichi sun kama dan bindiga bayan an yi kukan kura an kama shi da kayan sojoji.
Rundunar 'yan sandan Kano ta tabbatar da cewa mutanen karamar hukumar Bichi sun kama dan bindiga bayan an yi kukan kura an kama shi da kayan sojoji.
Yakubu Dogara ya musanta rahotannin cewa zai fice daga APC saboda tikitin Musulmi da Musulmi, yana mai tabbatar da goyon bayansa ga Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Gwamna Alia na jihar Benuwai ya ce duk mai hannu a mummunan harin da ya yi ajalin mutum 11 ba zai tsira ba, zai tabbatar doka ta yi aiki a kansa duk daren daɗewa.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'azziyarsa bayan rasuwar mahaifiyar Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa da dansa a wannan mako.
Shugaba Bola Tinubu ya yi sallar Jumu’a a masallacin Lekki inda Sheikh Ridhwan Jamiu ya yi addu’a domin nasararsa tare da kira gare shi da ya kasance mai adalci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun hallaka Rabaran Tobias Chukwujekwu Okonkwo a jihar Anambra bayan mummunan harin da aka kai masa a jiya Alhamis.
INEC na shirin lalata katunan zaɓe da ba a riga da an karɓa ba, inda za ta maye gurbinsu da fasahar BVAS don sauƙaƙe tantance masu zaɓe da tabbatar da ingancin zaɓe
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, Clement Adesuyi Haastrup ya zama sabon sarki a masarautar Ijesa a matsayin Owa-Obokun bayan kada kuri'a kan nadin.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kai farmaki wata maboyar barayi da suka sace Keke Napep a Danbatta. An mika Keke Napep din ga mai ita bayan bincike.
Tsohon kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Kwara, Alhaji Abdulrahim Adisa ya kwanta dama, ya rasu yana da shekaru 91 a duniya ranar Alhamis.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta addinin musulunci (MURIC) ta ce bai dace jami'an gwamnati su rika kalamai a kan addinin musulunci ba tare da ilimi ba.
Labarai
Samu kari