Mataimakin babban hafsan rundunar tsaron Birtaniya, Laftanar Janar Sir Charlie Collins, ya isa Maiduguri, babban birnin Borno a wata ziyara da ya kawo Najeriya.
Mataimakin babban hafsan rundunar tsaron Birtaniya, Laftanar Janar Sir Charlie Collins, ya isa Maiduguri, babban birnin Borno a wata ziyara da ya kawo Najeriya.
Iyalai da 'yan uwa da abokna arzikin malamar Islamiyya mai suna Ummulkhairi da aka kashe a Kaduna sun nuna matukar damuwa game da kisan da aka mata.
Yan bindiga sun kashe wasu daga cikin mutane fiye da 50 da suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya duk da karbar miliyoyin kudin fansa.
Wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun yi awon gaba da wasu mutane a jihar Neja. 'Yan ta'addan sun sace mutanen ne bayan sun kai farmaki a kauyensu.
Ana zargin Abubakar Ijidai ya kai hari kan tsohuwar budurwarsa da mahaifiyarta a gona, ya kashe mahaifiyar, sannan ya tsere. ‘Yan sanda na ci gaba da bincike.
An samu wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja. Lamarin ya auku me bayan wani jirgi da yake dauke da fasinjoji ya kife a tsakiyar kogi yana cikin tafiya.
Kungiyar Limamai da Alarammomi ta Ogun ta nuna damuwa kan hana zirga-zirga da ake shirin kakabawa a Ikolaje da Idiroko saboda jana’izar sarki da ya rasu.
Tinubu ya nada shugabanni a hukumomin tarayya 42 a shekarar 2025. Manufar hakan ita ce inganta shugabanci da samar da aiki ta hanyar wakilcin kowane yanki.
Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta shawarci matasan yankin Arewa da su yi taka tsan-tsan da madugun Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Yan bindiga sun kai wani hari yayin da suka sace wani Fasto da wasu biyu a gonarsu da ke Bauda a Maro da ke cikin Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka jagororin 'yan bindiga a jihar Sokoto. Sojojin sun kashe bata garin ne bayan sun yi musu kwanton bauna.
Labarai
Samu kari