Rundunar 'yan sandan Benue ta kama mutum 10 da ake zargi da kashe shugaban MACBAN na Benue, Alhaji Ardo Risku Mohammed, tare da abokinsa Yakubu Isah.
Rundunar 'yan sandan Benue ta kama mutum 10 da ake zargi da kashe shugaban MACBAN na Benue, Alhaji Ardo Risku Mohammed, tare da abokinsa Yakubu Isah.
Kasashen duniya 142 ciki har da Najeriya sun goyi bayan kafa kasar Falasdinawa a Gaza duk da adawar da Isra'ila da Amurka suka nuna a majalisar dinkin duniya.
Ministar harkokin mata Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana cewa ba ta rike kowane ma'aikaci a zuciya ba kan zanga-zangar da suka gudanar a kanta.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da gaggauta yin shari'ar dan Najeriya da ya kai hari ofishin majalisar dinkin duniya. An kama Khalid Al-Barnawi a 2016.
Hukumar Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi ta tabbatar da rasuwar dalibar ND II, Barira Adam a dakin kwanam dalibai mata bayan fama da jinya.
Tsohon ɗan takarar gwamna a jam'iyyar SDP a jihar Kogi, Muritala Ajaka, ya yi alhininsa kan rasuwar Sarkin Elaite yana cewa marigayin mutum ne mai son zaman lafiya.
Yan asalin Isara Remo da ke zaune a kasashen waje da wadanda ke gida sun hada kai sun yi fatali da wanda aka zaba a matsayin sabon Sarkinsu a jihar Ogun.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tura kudiri a gaban majalisar dokoki kan auren jinsi. Kudirin ya kuma shafi munanan dabi'u na madigo da liwadi.
Tawagar 'yan Najeriya mazauna Faransa sun ba Sanata Rabiu Musa Kwankwaso lambar yabo saboda yadda ya ke tallafawa mutane da tallafin karatu a Kano.
Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa bude boda domin shigo da kayan abinci ya karya farashin abinci a Najeriya, ya ce an karfafi manoma.
Labarai
Samu kari