Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada belin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore. Alkalin kotun ya gindaya masa sharudda.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada belin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore. Alkalin kotun ya gindaya masa sharudda.
Bayan shekaru 50, gwamnatin tarayya ta yi wasu gyare-gyare a tsarin NYSC. Sabon tsarin ya zo da rage karfin sojoji, kokarin koyar da sana'o'in zamani da kyau.
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), ya tabo batun illar da yajin aikin kungiyar manyan ma'aikatan man fetur na kasa (PENGASSAN) ya jawo a kasa.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da sace kansiloli biyu a jihar da kuma wani limami bayan idar da sallar mangariba.
Tsohon Shugaban Hukumar NBS na kasa, Yemi Kale ya ce Najeriya ce kasa ta 2 a jerin kasashen da suka fi yawan talakawa a duniya, ya bukaci a tashi tsaye.
Yayin da an bindiga suka addabi jihar Kwara a Arewacin Najeriya, gwamnatin ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin jagororin masu garkuwa da mutane, Maidawa.
Sojojin 6 Brigade sun dakile harin ‘yan ta’adda a Taraba, sun halaka biyu tare da kwace makamai, yayin da rundunar ke ci gaba da Operation Lafiya Na Kowa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi muhimmin kira ga 'yan Najeriya. Shugaba Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su daina yin kalamai marasa kyau a kan kasar.
Gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta tura sakon ta'aziyya bayan babban rashin tsohon kwamishina, Julius Ishaya Lepes.
Rashin tsaro da ya hada da hare haren 'yan bindiga ya tilasta rufe makarantu 188 a Arewacin Najeriya. An rufe makarantu a Katsina, Zamfara Neja da Zamfara.
A labarin nan, za a ji gwamnatin tarayya ta karyata ikirarin Peter Obi na cewa manufofin Bola Tinubu sun jefa jama'a a cikin mawuyacin hali da talauci mai tsanani.
Labarai
Samu kari