'Yan Bindiga Sun Je har Gida Sun Harbe Shugaban Miyetti Allah
- 'Yan bindiga da ake zargi da zama ɓarayi sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba
- Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne a gidan shugaban wato Ibrahim Saidu a daren Lahadi bayan sun iso a kan babura
- Rundunar ta yi kira ga iyalan mamacin da al'umma da su kwantar da hankulansu don gudun ɗaukar doka a hannu ko harin ɗaukar fansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba – Wasu tsagerun ɓarayin daji da ake zargi sun kashe shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na ƙaramar hukumar Takum da ke jihar Taraba, Ibrahim Saidu.
Kakakin rundunar ƴan sanda ta jihar Taraba, Victor Mshelizah, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce an harbe Saidu ne a gidansa ranar Lahadi.

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito bayan shekaru 5, kotu ta sallami wanda ake zargi da kashe matarsa a Kano

Source: Facebook
The Cable ta rahoto cewa a cewar Mshelizah, binciken farko ya nuna cewa maharan sun zo ne a kan babur kafin su aiwatar da harin.
Bayanin da 'yan sanda suka yi
Mshelizah ya bayyana cewa rundunar ta fara bincike domin gano ainihin dalilin da ya sa aka tafka wannan danyen aiki da kuma kamo waɗanda ke da hannu domin fuskantar shari'a.
Ya rubuta cewa:
“Rundunar tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa tsaro a yankin da abin ya shafa da kuma hana wargajewar doka da oda.”

Source: Original
Kakakin ƴan sandan ya yi kira ga mazauna yankunan da abin ya shafa, musamman iyalan mamacin, abokan hulɗarsa, da magoya bayansa da su kwantar da hankulansu su kuma guji matakan da ka iya taɓarɓare lamarin ko ɗaukar mafari.
Karin bayani daga 'yan sanda
Haka zalika, ya roƙi al'umma da su guji yaɗa jita-jita ko bayanan da ba a tabbatar ba waɗanda za su iya ruguza binciken da ake gudanarwa ko kuma shafan zamantakewar lafiya.
A wani sako da rundunar 'yan sandan ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce:
“Duk wanda ke da ingantaccen bayani da zai taimaka wajen gudanar da bincike, ana ƙarfafa masa gwiwa da ya tuntubi ƴan sanda ko sauran hukumomin tsaro.”
Kalu ya sayar da makamai
A wani labarin, kun ji cewa Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa ya taɓa yin sana'ar sayar da manyan makamai a matakin ƙasa da ƙasa ga duk wanda ke da kuɗin saya kafin iyayensa su sa shi ya bar sana'ar.
Kalu ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin, lokacin da yake magana kan sana'o'insa na baya da kuma alaƙarsa da shugabannin ƙasar Afirka ta Kudu.
Da aka tambaye shi ko shi ɗan kasuwar makamai ne, tsohon gwamnan jihar Abia ya amsa da eh, yana mai cewa ya bar sana'ar ne bayan mahaifiyarsa da mahaifinsa sun shiga tsakani.
Asali: Legit.ng
