Bidiyon Yadda Aka Tallafa wa Tinubu Yana Tafiya a Wurin Taro Ya Dauki Hankali, Sowore Ya Yi Magana

Bidiyon Yadda Aka Tallafa wa Tinubu Yana Tafiya a Wurin Taro Ya Dauki Hankali, Sowore Ya Yi Magana

  • Omoyele Sowore ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da koshin lafiya bayan ganin yadda aka rika rike shi yayin tafiya a wurin kamfen a Rivers
  • Dan takarar shugaban kasar na AAC ya ce Tinubu da alama ba zai iya kula da harkokinsa na kansa ba, balle ya jagoranci Najeriya
  • Sowore ya zargi mutanen da ke amfana da halin da ya ce shugaban ke ciki da rashin kishin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya jaddada zargin da ya yi a baya cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da lafiya.

Sowore, wanda ya shahara a harkokin gwagwarmaya da kare hakkin dan adam, ya yi ikirarin cewa Tinubu ba shi da kargi da lafiyar ci gaba da jagorantar kasar nan.

Kara karanta wannan

"Na ƙara gane rayuwa," Sanata ya ɗauko muhimman darussa a zaman da ya yi a gidan yari

Sowore.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zaben 2027, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Dan gwagwarmayar ya bayyana haka tare da wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook X ranar Talata, 10 ga watan Nuwamba, 2026.

Sowore ya zargi Tinubu da rashin lafiya

A gajeren bidiyon, An ga yadda jami'an tsaro suke rike Tinubu ta yana tafiya, lamarin da ya ja hankali kan halin da shugaban kasar ke ciki sakamakon ganin yadda ya gaza tafiya shi kadai.

Da yake martani, dan rajin kare hakkin dan Adam, Omoyele Sowore, ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da koshin lafiya, bayan ganin yadda aka rika rike shugaban yayin da yake tafiya a wani taron kamfen a Jihar Rivers.

Sowore ya dage cewa Tinubu ba shi da cikakkiyar lafiya, yana mai cewa shugaban ba zai iya kula da harkokinsa na kansa ba, balle ya jagoranci kasa mai bukatar shugabanci mai kuzari.

Ya kafa hujja da bidiyon Tinubu

Ya kuma zargi mutanen da yake ganin suna cin moriyar abin da ya kira tabarbarewar lafiyar Tinubu ta bangaren tunani da karfin jiki da rashin kishin Najeriya.

Kara karanta wannan

An ɗauki bidiyon jagoran jam'iyyar su Kwankwaso ya tuɓe kaya ya shiga kogi

A kalamansa, Sowore ya ce:

“Ina nan kan baka ta cewa wannan mutumin ba shi da koshin lafiya kwata-kwata, kuma ba zai iya kula da harkokinsa na kansa ba, balle ya jagoranci kasa da ke matukar bukatar shugabanci mai kuzari.
“Mutanen da ke cin moriyar tabarbarewar lafiyarsa ta bangaren tunani da karfin jiki ba su da kyakkyawar manufa ga Najeriya, amma ba za su iya boye gaskiya har abada ba. Tinubu ba shi da lafiya!”

Maganganun Sowore sun biyo bayan wani yanayi da aka gani a wajen kamfen a Rivers, inda aka rika taimaka wa Tinubu ta hanyar rike shi yayin tafiya.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin yakin neman zabe a Rivers Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sai dai kalaman Sowore na nuna ra'ayinsa ne kan yanayin shugaban, ba tabbacin likita ko rahoton hukuma da ya tabbatar da cewa Tinubu na fama da wata cuta ba.

Da gaske Tinubu ba shi da lafiya?

Kun ji cewa Nentawe Yilwatda ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan lafiyar Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasar yana da ƙoshin lafiyar da zai iya tsayawa takara.

Shugaban APC ya ce rashin halartar Tinubu wasu tarukan yaƙin neman zaɓe ba yana nufin gazawa ko rashin ƙarfin jagoranci ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262