An Samu Matsala: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Cire Kansa daga Shirin Su Atiku a 2027
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce ba zai shiga haɗakar ’yan adawa da ake shirin kafawa ba
- Sowore, fitaccen dan gwagwarmayar karr hakkin dan adam, ya yi hasashen cewa haɗakar za ta wargaje bayan babban zaɓen 2027
- Ya kuma nemi a bai wa sauran jam’iyyun siyasa damar amfani da Aso Rock wajen gudanar da harkokin siyasa kamar jam’iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya yi watsi da shirin shiga haɗakar jam’iyyun adawa, inda ya yi hasashen cewa haɗakar za ta rushe bayan babban zaɓen shekarar 2027.
Sowore ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a wani taro da Cibiyar Ƙwararrun Akantoci ta Najeriya (ICAN) ta shirya.

Source: Facebook
Ya soki shirin haɗakar, inda ya bayyana ta a matsayin wani tsari na wucin gadi wanda ba zai daɗe ba bayan zaɓen da ke tafe, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
“Ba na son kasancewa cikin haɗakarku saboda na san haɗakar da kuke shirin kafawa za ta mutu bayan 2027. Ba ni da ko tantama a kan hakan,” in ji shi.
Sowore ya soki haɗakar ’yan adawa
Ɗan takarar na AAC ya kuma nuna shakku kan dalilin da ya sa ’yan siyasar jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa kai, yana mai cewa irin wannan tsari ba zai samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin da ’yan Najeriya ke fuskanta ba.
Ya ƙara da sukar masu rike da madafun ikon siyasa, inda ya ce al’ummar ƙasar na fuskantar matsanancin ƙuncin tattalin arziki.
“Ko an yi shi a Fatakwal, ko a Legas, ko kuma a Jihar Osun, kowa ya san sun kawo baƙin ciki, kuma a gaskiya, rayuwa ta yi tsanani ga al’ummar wannan ƙasa,” in ji Sowore.

Kara karanta wannan
2027: Ana zargin wasu ƙusoshin APC sun fito da kudi don ruguza shirin hadewar yan adawa
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da wasu ’yan siyasa da jam’iyyun adawa ke ƙoƙarin haɗa kai domin tunkarar babban zaɓen 2027.
AAC ta nemi amfani da Aso Rock
Da yake magana kan harkokin siyasar jam’iyyarsa, Sowore ya bayyana cewa AAC ta nemi izinin amfani da Aso Rock wajen ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa.

Source: Facebook
A cewarsa, buƙatar ta samo asali ne daga hujjar cewa Aso Rock na ’yan Najeriya ne, don haka bai kamata a ɗauke shi a matsayin wurin da jam’iyya mai mulki kaɗai za ta riƙa amfani da shi ba.
“Mun nemi amfani da Aso Rock ne saboda APC tana amfani da wurin wajen gudanar da harkokin jam’iyya. Don haka, muna cewa a matsayinmu na masu haƙƙi, tunda Aso Rock namu ne, dole ne a bai wa sauran jam’iyyun siyasa damar amfani da shi kamar yadda APC take yi,” in ji shi.
Sowore ya zargi Peter Obi
Kun ji cewa Omoyele Sowore, ya zargi Peter Obi da jagorantar magoya bayansa a boye domin su yi wa Atiku Abubakar aiki a zaɓen 2027.
Sowore ya bayyana Obi a matsayin wanda yake yaudarar jama'a, yana mai zargin cewa yana tura magoya bayansa su yi wa Atiku aiki a ɓoye saboda sun yi hannun riga da manufofinsa na kawo sauyi.
Asali: Legit.ng
