'Karatun Ta Natsun Tinubu Ya Sa Shugaban Faransa Ya Soke zuwa Najeriya'
- Bashir Ahmad ya goyi bayan Shugaba Bola Tinubu kan rahoton soke ziyarar Emmanuel Macron Najeriya
- Ahmad ya ce damuwar Tinubu kan yiwuwar zargin katsalandan daga ƙasashen waje a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ta dace
- Rahotanni sun ce Macron da Tinubu sun amince da soke ziyarar saboda zanga-zanga a Faransa, zaɓen Najeriya da bullar Ebola
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, tsohon hadimin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan soke ziyarar shugaban Faransa a Najeriya.
Bashir Ahmad ya goyi bayan Shugaba Bola Tinubu kan rahoton soke ziyarar Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da aka shirya yi Najeriya gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Facebook
Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a 23 ga watan Oktobar 2026.
Macron: Bashir Ahmad ya yabi kokarin Tinubu
Matashin ya bayyana damuwar da ake cewa Tinubu ya nuna kan yiwuwar ziyarar Macron ta jawo zargin katsalandan daga ƙasashen waje a harkokin zaɓen Najeriya a matsayin matakin da ya dace.
Ya ce:
“An kuma ruwaito cewa Tinubu ya nuna damuwa kan cewa ziyarar Emmanuel Macron, watanni kusan uku kafin zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya, na iya jawo zargin tasirin ƙasashen waje. Wannan mataki ne da ya dace."

Source: Facebook
Emmanuel Macron ya soke ziyara zuwa Najeriya
Martanin Ahmad ya biyo bayan wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa, wanda ya ce Macron ya soke ziyarar aiki da aka shirya zai kai Najeriya ranar Laraba, 28 ga Oktoba.
Rahoton ya bayyana cewa an soke ziyarar ne sakamakon damuwa kan zanga-zangar da ake yi a Faransa, zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa a Najeriya da kuma sabon bullar cutar Ebola.
A cewar jaridar, wasu majiyoyin Najeriya da ke da masaniya kan shirin ziyarar sun bayyana cewa Macron da Tinubu sun amince da soke tafiyar a ranar Alhamis.
An ruwaito cewa Macron ya damu cewa zuwa Najeriya a lokacin da ake ci gaba da zanga-zanga a Faransa na iya bayyana a matsayin rashin kulawa da halin da ake ciki a ƙasarsa.
Zanga-zangar ta haifar da rufe makarantu, sace-sacen kayayyaki da kuma arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro.
Rahoton soke ziyarar ya zo ne watanni kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya na 2027, wanda Tinubu ke neman sake tsayawa takara domin samun wa’adi na biyu.
Seyi Tinubu ya kunyata Bashir Ahmad
A baya, kun ji cewa taohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya yi martani kan bidiyon da ke nuna Seyi Tinubu ya tsallake shi yayin gaisawa da mutane.
Bashir Ahmad ya bayyana cewa sun raka Seyi Tinubu ne domin ganawa da kungiyar mata, ba wai domin ganawa da shi kai tsaye ba.
Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda mutane da dama ke yi wa Bashir ba'a saboda yadda yake tallata APC da Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng

