‘Babu Dan Hassada Kamar Pantami’: Malamin Musulunci Ya Fusata Kan Siyasa

‘Babu Dan Hassada Kamar Pantami’: Malamin Musulunci Ya Fusata Kan Siyasa

  • Matashin malamin Musulunci ya nuna takaici kan yadda wasu magoya bayan Farfesa Isa Ali Pantami ke sukar masu masu adawa
  • Malamin ya ce rashin goyon bayan Pantami ba yana nufin mutum yana yi masa hassada ba, domin kowa na da damar bin ra'ayinsa
  • Alaranman ya bayyana goyon bayansa ga Jamilu, yana mai ƙalubalantar masoyan Pantami da su kawo hujjar da ta tilasta wa kowa goyon bayansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Siyasar jihar Gombe na ci gaba da daukar zafi yayin da aka sake dawo da Farfesa Isa Ali Pantami domin yin takara.

Alaranma Ismail Maiduguri ya fusata kan yadda wasu magoya bayan Pantami ke kiran masu adawa da shi a matsayin masu hassada.

Ismail Maiduguri ya soki Pantami
Farfesa Isa Ali Pantami da Alaranma Ismail Maiduguri. Hoto: Professor Isa Ali Pantami, Ismail Maiduguri.
Source: Facebook

Ismail Maiduguri ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da wakilin Legit Hausa ya bibiya wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya kuma magana, ya ba Tinubu shawarar da za ta taimaki gwamnatinsa

Malamin Musulunci ya fusata da yan Pantamiyya

Ismail ya nuna takaici yadda ake kiransu da masu hassada kawai don ba su goyon bayan Pantami a siyasar jihar Gombe.

Ya ce:

"Idan rashin goyon bayan Pantami shi ne hassada, to shi ya fara yi wa Jamilu hassada da ya ki goya masa baya, duk da suna jam'iyya daya.
"Pantami ya fi mu kusanci da Jamilu tun da jam'iyyarsu daya, ya ce suna iyayen APC kenan ma'aunin mahaukata kan hassada irin naku to Pantami ya fi kowa hassada.
"Ya za ku mayar da mu bayinku, da shekarunmu da yaranmu ku rinka cewa muna hassada domin hana mu fadar yancinmu, doka ce ta ba kowa damar son wanda ya ke so."
Alaranma Ismail Maiduguri ya soki masoyan Pantami
Alaranma Ismail Maiduguri yana daga cikin masu adawa da Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Ismail Maiduguri.
Source: Facebook

Kalubalen Ismail ga yan Pantamiyya

Matashin malamin ya kalubalanci masoyan Pantami da su kawo aya da ta ce dole ne sai an goyi bayansa a siyasar da ake yi.

Ya nuna takaici yadda suke dauka rashin goyon bayan Pantami a matsayin hassada inda ya ce kenan shi ma Pantami yana yi wa Jamilu hassada.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Tinubu ya fada kan zabe bayan shiga dakin Ka'aba a Saudi

"Ko kuma aya ce ta sauko cewa dole ne a goyi bayan Pantami, ku ba mu aya kan cewa dole ne a goyi bayan Pantami, idan babu aya to kyautata zato kuke yi ya fi shi, to nima Jamilu ya fi mun.
"Kenan duk wanda ba ya goyon bayan Atiku ko Tinubu ko Obi hassada ne, to kenan Pantami ma da baya goyon bayan Jamilu hassada ce."
Isma'il ya ce a ransa yana goyon bayan Jamilu kuma yana ganin ya fi Pantami, ya ce bai saba wa Allah ba, idan kuma suna shakku su kai shi kotu ko kai su wuta a lahira."

Ismail Maiduguri

Jamilu ya tura sako ga yan APC

A wani labarin, kun ji cewa dan takarar gwamnan Gombe na jam’iyyar APC, Jamilu Gwamna, ya bukaci ’yan jam’iyyar su kara himma wajen tallata shi a tsakanin al’umma.

A bayanin da ya yi, Jamilu Gwamna ya ce duk wanda ya gaza kawo akwatin mazabarsa ba zai kasance tare da shi ba bayan kafa gwamnati.

Ya kuma bukaci mambobin APC su tabbatar sun samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri’u sama da miliyan daya a zaben da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.