Tashin Hankali: Jirgin Kasa Ya Murkushe Wata Mota da Ta Biyo Ta Kan Titinsa a Najeriya
- Wani direba mai shekaru 55 ya tsallake rijiya da baya bayan jirgin ƙasa ya buge motarsa kirar Honda a layin dogo ta PWD da ke jihar Legas
- Hukumar LASTMA ta ce motar ta lalace sosai, amma jami’anta da jami’an tsaro sun ceto direban tare da cire motar daga kan layin dogo
- Hukumar ta gargaɗi masu ababen hawa da su kiyaye dokokin tsaron layin dogo tare da guje wa ƙoƙarin tsallaka layin lokacin da jirgin ƙasa zai wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Jirgin kasa ya yi awon gaba d wata mota kirar Honda yayin da zai wuce ta titinsa da ke PWD a jihar Legas.
An ruwaito cewa direban motar mai shekaru 55 ya tsira ba tare da rauni ba bayan jirgin ƙasa da ke tafiya ya buge motarsa, amma dai an ce motar ta yi kwatsa-kwatsa.

Source: Facebook
Leadership ta ruwaoto cewa Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa hatsarin ya haɗa da jirgin ƙasa da ke tafiya zuwa Agege da kuma motar Honda mai lambar rajista EKY 902 JT.
Hukumar ta ce jami’anta tare da jami’an tsaro sun ceto direban tare da cire motar da ta lalace daga kan layin dogo, lamarin da ya ba jirgin damar ci gaba da tafiyarsa.
Duk da cire motar, cunkoson ababen hawa ya ci gaba da faruwa a yankin PWD bayan hatsarin.
LASTMA ta ƙara da cewa daga bisani ta miƙa motar da ta lalace ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin.
LASTMA ta gargaɗi direbobi
Babban manajan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya yaba wa jami’an hukumar da jami’an tsaro bisa hanzarin da suka yi wajen kai ɗauki da haɗin gwiwar da suka nuna wajen shawo kan lamarin.
Ya ce matakin da suka ɗauka ya nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da abin ya shafa wajen tunkarar aukuwar haɗurra da suka shafi zirga-zirgar jiragen ƙasa da hanyoyin da ke kusa da layin dogo.
Bakare-Oki ya kuma buƙaci direbobi da su riƙa taka-tsantsan yayin da suke tunkarar mashigai da layukan dogo da aka ware domin zirga-zirgar jiragen ƙasa.
Ya gargaɗe su da kada su yi ƙoƙarin tsallaka layin dogo idan jirgin ƙasa yana gabatowa ko kuma yana tafiya.
Ya yi gargaɗin cewa, “yin watsi da ƙa’idojin tsaron layin dogo cikin ganganci na iya jawo mummunan sakamako da ba za a iya gyarawa ba.”
Hukumar ta kuma yi kira ga masu amfani da hanyoyi da su bi ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa da na tsaron layin dogo yadda ya kamata domin kauce wa haɗurran da za a iya hana faruwarsu.
LASTMA ta jaddada cewa “kare rayukan jama’a dole ne ya kasance babban abin la’akari a duk shawarar da ake yankewa yayin amfani da hanya.”
Hukumar ta ƙara da cewa tuƙi cikin kulawa da bin umarnin tsaro yadda ya kamata na da matuƙar muhimmanci wajen rage haɗurran da ke faruwa a mashigai da layukan dogo.
Asali: Legit.ng

