Tunji Ojo: Gwamnati Ta Shiga Binciken Ministanta da Ake Zargi a Badakalar Kwangila

Tunji Ojo: Gwamnati Ta Shiga Binciken Ministanta da Ake Zargi a Badakalar Kwangila

  • Hukumar CCB ta aika takardar gayyata zuwa ga Ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo
  • Za a nemi Minista ya yi bayani a kan zargin da ake yi masa na saba doka wajen karbar kwangilar N438m
  • An ba kamfanin Tunji-Ojo kwagila, amma ya kafa hujja da cewa ya yi murabus daga kamfanin tun a 2019

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar CCB ta aikawa Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, gayyata domin ayi bincike a game da shi.

Rahoton da Punch ta kadaita da shi ya tabbatar da jami’an CCB sun fara binciken Olubunmi Tunji-Ojo a halin yanzu.

Tunji Ojo
CCB za ta zauna da Bunmi Tunji Ojo Hoto: @OfficialABAT/@BTOofficial
Asali: Twitter

Betta Edu da Olubunmi Tunji-Ojo

Ana zargin tsohon kamfanin Ministan ya samu kwangila daga hannun Ministan jin-kai da yaki da talauci watau Betta Edu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Matawalle da sauran tsaffin gwamnoni 13 da EFCC ta sake waiwayar zargin badakala kansu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ita kan ta Dr. Betta Edu an dakatar da ita domin yin binciken kan zargin bada umarnin tura kudi zuwa wani asusu.

Tunji-Ojo da kamfanin New Planet Projects

Tun tuni aka taso takwaranta watau Tunji-Ojo a gaba ganin yadda ta ba kamfaninsa na New Planet Projects kwangila a 2023.

Wata takarda da jaridar ta ci karo da ita a ranar Litinin ya nuna CCBN ta nemi zama da ministan a ranar Talata 16 ga Junairu.

Za ayi wannan zama ne a hedikwatar CCB da ke sakatariyar ma’aikatun tarayya a Abuja.

Takardar binciken Tunji Ojo ta fito daga CCB

Darektan bincike da sa-ido a hukumar CCB, Gwimi S.P ya sa hannu a takardar a madadin shugabanta, Murtala Aliyu Kankiya.

Gayyatar kamar yadda takardar ta nuna, ta na cikin ikon da doka ta ba CCB a karkashin kundin tsarin mulkin Najeriyan 1999.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun adawa sun cigaba da shirin hada kai domin yakar Tinubu da APC a 2027

Takardar ta fadawa Tunji-Ojo cewa ana neman shi ne domin yin bincike a kan zargin sabawa ka’idojin aikin gwamnatin tarayya.

Gwimi S.P yake cewa sunan tsohon ‘dan majalisar yana yawo don haka ake neman shi.

Tunji-Ojo: Ana so a binciki Ministan gida

Mai girma ministan ya ce ya ajiye kujerarsa a kamfanin da ake magana, amma kamfanin yana karkashin mai dakinsa ne.

A baya rahotanni sun ce ‘ya ‘yansu ne darektocin kamfanin, saboda haka ake ganin bai tsira daga zargin sabawa ka’idar aiki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel