Gwamnan Bauchi ya nada hadima mai kula da harkokin zawarawa

Gwamnan Bauchi ya nada hadima mai kula da harkokin zawarawa

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya amince da nadin hadima da zata taimaka masa wajen gudanar da harkokin zawarawa na jihar. Wannan shine karo na farko da aka taba bayar da irin wannan mukami.

Gwamnan jihar ya amince da nada Balara Ibrahim, wacce ta fito daga karamar hukumar Ganjuwam bisa ga cancantarta da kuma goyon bayan da ta ke yiwa gwamnatin.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Muhammed Sabiu Baba, sakataren gwamnatin jihar, mai dauke da kwanan wata, 4 ga watan Agusta.

A cikin takardar, gwamnan jihar ya bukaci Balara Ibrahim, da ta zage damtse wajen gudanar da ayyukan ofishinsa, a kokarin gwmanatin na ganin ta tafi da kowa a shan romon demokaradiyya.

Yan wasa suyi hattara, domin kuwa za su iya samun jan kati daga alkalin wasa ma damar suka yi tari da gangan a fuskar wani dan wasan ko jami'an wasa.

KARANTA WANNAN: Ba sani ba sabo: Hukuncin da za ayiwa duk dan wasan da yayi tari a filin kwallo

Gwamnan Bauchi ya nada hadima mai kula da harkokin zawarawa
Gwamnan Bauchi ya nada hadima mai kula da harkokin zawarawa
Asali: UGC

A bangaren taka leda kuwa; kungiyar kwallon kafa ta turai tayi nuni da cewa cin fuskane yin tari ana tsakiyar annobar COVID-19.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta kasa da kasa (IFAB) ta ce ya ragewa alkalin wasan ya tantance ko anyi tarin don cin zarafi ko kuma ba da gan gan aka yi ba.

IFAB ta ayyana yin tari da gangan ga wani dan wasa a matsayin "cin zarafi, zagi ko amfani da kalaman batanci ko motsi mai nuna rashin da'a".

"Kamar yadda yake ga kowanne laifi, dole alkalin wasane zai yanke hukunci akan gaskiyar dalilin yin tarin," a cewar ta.

"Idan har ba da gangan bane, to alkalin wasa ba zai dauki mataki akan tarin da aka yi a tazara mai nisa tsakanin yan wasan ba.

"Amma idan har ta tabbata anyi tarin ne domin cin mutunci, to a nan alkalin wasa zai iya daukar mataki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel