Wani Gini Mai Dauke Da Dakuna 500 Ya Ruguje a Legas

Wani Gini Mai Dauke Da Dakuna 500 Ya Ruguje a Legas

  • Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya sanya wani ɓangare na wani gini da aka fi sani da Agboye Estate a Ketu, jihar Legas, ya ruguje
  • Ginin, wanda ke dauke da mutane da dama cikin ɗakuna sama da 500, da farko ya fara rugujewa a ranar Asabar sannan a ranar Lahadi, 17 ga Satumba
  • Mutane biyu sun raunata inda aka garzaya da su zuwa wani asibitin kuɗi, yayin da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas ta killace wurin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ketu, jihar Legas - Wani ɓangare na ginin wata makaranta da aka mayar wajen kwanan mutane da ke a unguwar Ketu a jihar Legas, ya ruguje

Jaridar Punch ta rahoto cewa ginin yana da ɗakuna sama da 500 tare da ɗaruruwan mazauna wanda aka fi sani da Agboye Estate da ke kan titin Oduntan, a unguwar Ketu.

Wani gini ya rufto a Legas
Wani gini mai dauke da dakuna 500 ya ruguje a Legas Hoto: @iam_fifty_fifty
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa ginin ya fara rugujewa ne da yammacin ranar Asabar bayan da aka kwashe sa’o’i ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, wanda ya mamaye mafi yawan sassan Legas.

A ranar Lahadi da yamma, yayin da mazauna wurin ke ci gaba da ƙoƙarin kwashe kayansu, ginin ya sake rugujewa, inda wani ɓangare na ginin ya lalace, kafin ya ruguje gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane biyu sun jikkata

Aƙalla mutane biyu ne suka jikkata kuma an garzaya da su zuwa wani asibitin kuɗi.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas ta killace ginin.

An tattaro cewa tuni dama jami'an gwamnatin jihar Legas, suka yi wa ginin wanda yake ɗauke da rubabin ɗakuna alamar ruguzawa.

Yadda gini ya rushe a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ginin otal mai hawa huɗu da ke a yankin Dape, Life Camp, a birnin tarayya Abuja ya ruguje.

Wani shaidar ganau ba jiyau ba wanda lamarin ya auku a kan idonsa ya bayyana cewa ginin ya kife kan mutane sama da 20.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2023 yayin da ma'aikata ke tsaka da aikin gina wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel