Sarkin Gombe, Abubakar III ya jinjinawa kokarin Osinbajo a tafiyar Gwamnatin Buhari

Sarkin Gombe, Abubakar III ya jinjinawa kokarin Osinbajo a tafiyar Gwamnatin Buhari

- Abubakar Shehu Abubakar III ya yabi Mataimakin shugaban Najeriya

- Sarkin Gombe ya yaba da rawar da Farfesa Yemi Osinbajo ya ke takawa

- Mai martaban ya ce Muhammadu Buhari ya yarda da mataimakin na sa

Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya amince da mataimakinsa, Yemi Osinbajo.

Abubakar Shehu Abubakar III ya ke cewa shugaban kasa ya na jin dadin Farfesa Yemi Osinbajo saboda nasarorin da aka samu a bangaren tattalin arziki.

Sarkin Gombe ya ce Farfesan ilmin shari’ar ya kawo cigaba a shekaru shida da su ka yi a mulki. The Nation ce ta fitar da wannan rahoto a ranar Laraba.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta sa ranar kammala titin Abuja - Kano

Basaraken ya yi magana ne a ranar Talata, 30 ga watan Maris, 2021, lokacin da mataimakin shugaban Najeriyar ya kai masa ziyara a fadarsa a Gombe.

Da yake magana da Yemi Osinbajo, Sarkin ya ce: “Ziyararka a yau ta tabbatar da kokarin gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Muhammadu Buhari, da goyon-bayan da ka ke ba mutanenmu."

Shehu Abubakar III ya cigaba da cewa: “Ina so in yaba wa gwamnatin tarayya saboda kokarinta na kawo cigaban tattalin arziki ga mutanenmu, musamman a bangaren aikin gona da kananan sana’o’i.”

“Gombe jiha ce da ta dogara da noma, kuma matattarar kasuwanci a Arewa maso gabas.”

KU KARANTA: Ba za mu manta da talakawa da nakasassu ba - Buhari

Sarkin Gombe, Abubakar III ya jinjinawa kokarin Osinbajo a tafiyar Gwamnatin Buhari
Sarkin Gombe da Yemi Osinbajo Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

“Zuwan kai yau, ya zo daidai da matsayinka na direban tattalin arzikin kasar nan, a matsayinka na shugaban majalisar tattalin arziki, ka kawo gyare-gyare a harkar saukin kasuwanci, fasahar zamani, da kuma manufofin da su ka rage radadin COVID-19.”

“Wannan ya nuna matsayinka a gwamnatin Buhari, da yadda shugaban kasa ya yarda da kai.

“Mu a Arewa mu na biye da nasarorin da ka ke samu a kai-a ka; na farko nasarar zaman ka Farfesa, jagoran addini, sannan kuma mataimakin shugaban Najeriya.”

A ranar Laraba ne Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya caccaki Gwamnatin Muhammadu Buhari a fakaice, ya ce shi ba zai tafi ketare domin a duba masa lafiya ba.

Gwamna Wike ya ke cewa babu abin da zai ki shi asibitin kasar waje domin su na da komai a Jihar Ribas. Wike ya bayyana wannan a lokacin da Buhari ya tafi Ingila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel