An Yi Rashi: Mutumin da Ya Fara Shigar da Tinubu cikin Harkokin Siyasa Ya Mutu

An Yi Rashi: Mutumin da Ya Fara Shigar da Tinubu cikin Harkokin Siyasa Ya Mutu

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar Alhaji Ganiyu Oseni, mutumin da ya kira jagora, aboki kuma wanda ya fara shigar da shi siyasa
  • Tinubu ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasararsa ta zama sanatan Legas ta Yamma da kuma gwamnan Legas
  • Shugaban ƙasar ya yabawa Oseni kan gwagwarmayar kare nasarar zaɓen 12 ga Yuni da kuma fafutukar dawo da dimokuraɗiyyar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar fitaccen ɗan siyasa kuma dattijon jihar Legas, Alhaji Ganiyu Kolapo Oseni.

Shugaban kasar na Najeriya ya bayyana Alhaji Oseni a matsayin jagora, amini, ɗan uwa kuma mutumin da ya fara shigar da shi harkokin siyasa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar Alhaji Ganiyu Oseni.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na duba wasu takardu a ofishinsa. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya tuno da rayuwar Alhaji Oseni

A cikin wata sanarwar ta'aziyya da ya fitar a shafinsa na X a ranar Juma'a, Tinubu ya ce rasuwar Oseni babban rashi ne gare shi da kuma Najeriya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Dan a mutun Tinubu ya kare Oluremi, ya ba da labarin attajira mai sayar da ƙosai a Abuja

Shugaban ƙasar ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen shugaba, ɗan siyasa mai kishin ci gaba da kuma jajirtaccen mai hidimar jama'a wanda ya bar tarihi mai kyau a jihar Legas da Najeriya.

A cewarsa, Oseni ya yi aiki a matsayin sakataren tsare-tsare na jam'iyyar UPN a jihar Legas a zamanin Jamhuriya ta Biyu ƙarƙashin jagorancin marigayi Cif Obafemi Awolowo.

Ya kuma taka rawa wajen kafa kamfanin buga takardu na gwamnatin jihar Legas.

"Oseni ya shigar da ni siyasa" - Tinubu

Tinubu ya ce Oseni ya fi zama jagora a gare shi fiye da matsayin aboki kawai, yana mai cewa:

"Shi ne ya shigar da ni siyasa, kuma tare da wasu ya tsaya a bayana har na zama sanatan Legas ta Yamma, daga baya kuma gwamnan jihar Legas."

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa ba zai taɓa manta irin sadaukarwar da suka yi tare ba wajen fafutukar dawo da dimokuraɗiyya a Najeriya.

Tinubu ya bayyana Oseni a matsayin gwarzon dimokuraɗiyya wanda ya yi gwagwarmaya domin kare sahihancin zaɓen 12 ga Yuni da marigayi Bashorun Moshood Abiola ya lashe.

Shugaba Tinubu ya ce marigayi Oseni ya taka rawa wajen kafa gwamnatinsa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zaune a ofis. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Alakar Oseni da gwamnatin Tinubu

Kara karanta wannan

"Obi ya ci amana ta," Sabon mai magana da yawun Atiku ya tada hazo ana shirin zabe

Ya ce sun yi aiki tare wajen kawo ƙarshen mulkin soja da kuma tabbatar da dimokuraɗiyya ta samu gindin zama a ƙasar.

Tinubu ya kuma bayyana cewa marigayin ya mara masa baya tare da yi masa addu'a lokacin da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2022, duk da cewa a lokacin yana zaune a Amurka.

Shugaban ƙasar ya ce wasu daga cikin manufofi da gyare-gyaren da gwamnatinsa ke aiwatarwa a yau suna daga cikin ra'ayoyin da shi da marigayin suka tattauna domin inganta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com