Abdul Samad Rabiu BUA Zai Sayi Kungiyar Kano Pillars? An Ji Gaskiyar Zance

Abdul Samad Rabiu BUA Zai Sayi Kungiyar Kano Pillars? An Ji Gaskiyar Zance

  • An yada wasu rahotanni masu nuna cewa shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, zai sayi kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars
  • Kamfanin BUA ya fito ya yi martani kan rahotannin wadanda ya bayyana a matsayin marasa tushe ballantana makama
  • Rahotannin dai sun yi ikirarin cewa hamshakin attajirin zai sayi kaso 70 cikin 100 na kungiyar wadda ke taka leda a gasar NPFL ta Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kamfanin BUA (BUA Group) ya yi magana kan rade-radin cewa shugabansa, Abdul Samad Rabiu, zai sayi kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Kamfanin BUA ya yi watsi tare da karyata rahotannin da ke cewa Abdul Samad Rabiu, ya ƙaddamar da tayin neman sayen mafi rinjayen hannun jari a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Abdul Samad Rabiu ya yi magana kan sayen Kano Pillars
Abdul Samad Rabiu da wasu 'yan wasan kungiyar Kano Pillars Hoto: Abdul Samad Rabiu, CFR, CON, Kano Pillars FC
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin ya sanyawa hannu a ranar Litinin, 29 ga watan Yunin 2026, wadda aka sanya a shafin X.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja

Me BUA ya ce kan sayen Kano Pillars?

Babban kamfanin ya bayyana cewa duka kamfanin ko shugabansa ba su da wata manufa ko kuma wata tattaunawa da ke gudana domin sayen kashe 70 cikin 100 na hannun jari a ƙungiyar da ke fafatawa a gasar firimiya ta Najeriya (NPFL).

Kamfanin BUA ya bukaci daukacin jama'a da masu ruwa da tsaki da su yi watsi da waɗannan rahotanni baki ɗaya da cewa ba daidai ba ne kuma ba su da tushe balle makama.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Hankalinmu ya karkata zuwa ga wani labari da aka wallafa a yanar gizo wanda ke nuna cewa kamfanin BUA da shugabansa, Abdul Samad Rabiu, sun ƙaddamar da tayin sayen kashi 70 na hannun jari a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars."
“Muna son bayyana cewa wannan rahoto ba daidai ba ne kuma ba ya nuna kowane irin matsayi, mataki, ko magana daga kamfanin BUA ko Abdul Samad Rabiu. Babu irin wannan tayin da aka yi, kuma ba a yi wata tattaunawa da kowace ƙungiya ko mutum ba a kan wannan batu.”

Kara karanta wannan

'Ku kara hakuri,' manoma sun fadi lokacin da tumatir zai yi araha a Najeriya

Kamfanin BUA ya bada shawara

Babban kamfanin masana'antun ya ƙara shawarar kafofin yaɗa labarai da jama'a da su riƙa tantance bayanai game da ayyukansa ta hanyar amfani da sahihan hanyoyin sadarwarsa a hukumance da aka tabbatar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Muna buƙatar da a yi watsi da wannan rahoto, kuma muna ƙarfafa jama'a da mambobin kafofin yaɗa labarai da su dogara kawai ga bayanan da ake fitarwa ta hanyoyin sadarwa na kamfanin BUA da aka tabbatar domin samun ingantattun bayanai game da ayyukanmu."
BUA ya musanta batun sayen Kano Pillars
Yan wasan Kano Pillars na yin atisaye Hoto: Kano Pillars FC
Source: Facebook

Dukiyar Abdul Samad BUA ta karu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshakin dan kasuwa kuma attajiri a Najeriya, Abdul Samad Rabiu BUA, ya samu gagarumin kari a dukiyarsa.

Abdulsamad Rabiu ya zama mutum na biyu mafi arziki a nahiyar Afrika bayan samun gagarumar ƙaruwa a dukiyarsa cikin shekarar 2026.

Masana tattalin arziki na danganta ƙaruwar dukiyar Abdulsamad Rabiu, da irin gagarumar nasarar da kamfanin BUA Foods ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng