Valentine: An Raba Wa Ma'aikata Kyautan Kororon Roba a Bikin Ranar Masoya a Osun

Valentine: An Raba Wa Ma'aikata Kyautan Kororon Roba a Bikin Ranar Masoya a Osun

  • Ma'aikatan jihar Osun sun shiga sahun mutane da dama da suka yi bikin ranar masoya ta duniya (Valentine) da aka saba yi duk ranar 14 ga watan Fabrairu
  • Wani abu mai jan hankali a bikin ranar masoyan na bana a Osun shine yadda Ma'aikatan Lafiya na Jihar ta raba wa ma'aikatan kororon roba kyauta a wurin bikin
  • Bikin da aka gudanar a Sakatariyar Gidan Gwamnatin Osun ya samu halartar manyan baki ciki har da gwamnan jihar Ademola Adeleke wanda ya tura wakili tare da isar da sakonsa

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Osun - Mutane da dama a wurin bikin ranar masoya da Kungiyar Ma'aikatan Jihar Osun ta shirya a ranar Laraba sun samu kyautan kororon roba daga jami'an Ma'aikatan Jihar Lafiya.

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

Mahalarta taron da aka yi a Sakartariyar Gidan Gwamnatin Osun sun yi gasar rawa da wasu wasanni daban-daban kuma an bai wa zakarun kyaututuka.

Ma’aikatan, wadanda suka nuna himma a lokacin da aka raba kayayyakin, sun samu kwaroron roba na maza da mata kamar yadda The Punch ta rahoto.

Da ya ke magana da manema labarai, shugaban shirin kayyade iyali na jihar, Ololade Abatan, ya ce an raba kororon roban ne a matsayin wani tsari na kiyaye yaduwar cututtuka da ke yaduwa ta hanyar jima'i da daukan cikin da ba a so ba.

Abatan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duba da ni'imar da Allah ya mana na ganin ranar masoya na wannan shekarar, ya kamata mu kare kanmu daga cututtuka da ake yadawa ta hanyar jima'i kuma shi yasa muka zo nan mu rabawa mata da maza kororron roba.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama masu laifi 400 a jihar APC

"Mu fara amfani da kororon roba don kare kanmu daga cuttuka da ake dauka ta hanyar jima'i da cikin da ba a so ba. Dukkanmu zai yi wa amfani. Matasa da dattawa, ya kamata mu kare kanmu daga cututtukan da ake dauka daga saduwa."

Sakon gwamna na ranar masoya

A bangarensa, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, yayin jawabi wurin taron ya jadada bukatar da ke akwai na samun zaman lafiya da hadin kai a cikin al'umma da gwamnati saboda bikin ranar masoya.

Adeleke, wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan jihar, Ayanleye Aina, cikin sanarwar da kakakinsa, Olawale Rasheed, ya fitar ya yi kira ga al'ummar jihar sun rungumi kauna tare da yafewa juna kura-kuren da suka yi.

Jerin Kasashe 8 da Suka Haramta Yin Bikin Ranar Masoya

Ba boyayyen abu bane ga mafi yawan al'umma cewa an ware ranar 14 ga watan Fabrairu a matsayin ranar masoya na duniya.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

Kasashe da dama na duniya su kan yi bikin inda za a ga masoya suna yin abubuwa na musamman don nunawa mutanen da suke kauna a rayuwa muhimmancinsu.

Wasu na siyan kyaututuka su bayar, wasu kuma suna shirya zuwa yawon bude ido ku wuraren cin abinci tare da mosoya ko wani abu mai kama da hakan.

Amma duk da hakan akwai wasu kasashen duniya da ba a yin bikin ranar masoyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel