Ana Batun Bashin da Ake Bin Najeriya, Tinubu Ya Sa Hannu kan Yadda Za a Kashe N68.32tn a 2026
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar kasafin kudin shekarar 2026, wacce za ta lakume N68.32tn
- Bayan haka kuma Tinubu ya sa hannu kan kudirin tsawaita wa'adin aiwatar da kasafin kudin 2025, daga watan Maris, zuwa 1 ga watan Yulin 2026
- Mai girma shugaban kasa ya gode wa Majalisar dokoki bisa hadin kansu, tare da bai wa yan Najeriya tabbacin samar da ayyukan ci gaba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan dokar kasafin kudin shekarar 2026 wadda ta kai jimillar kudade Naira tiriliyan 68.32.
Haka kuma ya amince da karin wa’adin aiwatar da kasafin 2025 daga ranar 31 ga Maris, 2026 zuwa 30 ga Yuni, 2026.

Source: Twitter
Yadda za a kashe N68tn a 2026 a Najeriya
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, 17 ga watan Afrilu, 2026.
Kasafin kudin na shekarar 2026 ya ware Naira tiriliyan 4.799 domin biyan kudaden wajibi na doka, yayin da aka tanadi Naira tiriliyan 15.8 domin biyan bashin gwamnati.
An kuma ware Naira tiriliyan 15.4 na tafiyar da harkokin gwamnati na yau da kullum, yayin da aka ware Naira tiriliyan 32.2 domin ayyukan gina kayayyakin more rayuwa.
Kasafin ya nuna cewa kusan kashi 50 na kudaden an ware su ne domin ayyukan ci gaba, wanda ke nuna kudirin gwamnati na tabbatar da daidaiton tattalin arziki, tsaro, bunkasa ababen more rayuwa da kuma ci gaban jama’a baki daya.
Karin wa’adin kasafin 2025
Bugu da kari, shugaban kasar ya kuma rattaba hannu kan gyaran dokar kasafin 2025, wanda ya tsawaita wa’adin aiwatar da ayyukan da ke ciki daga ranar 31 ga Maris zuwa 30 ga Yuni, 2026.
An bayyana cewa wannan karin wa’adi zai bai wa gwamnati damar kammala muhimman ayyuka da ke gab da a kammala su a sassa daban-daban na Najeriya.
Tinubu ya umarci ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyi na gwamnati da su tabbatar sun yi amfani da kudaden da aka ware cikin gaskiya, tsari da kuma inganci.
Shugaba Tinubu ya godewa Majalisa
Shugaban kasar ya yabawa shugabanni da ‘yan majalisar dokoki ta kasa kan kokarinsu da hadin kai wajen duba da amincewa da kasafin cikin gaggawa.
Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da hadin kai tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa domin cimma manufofin ci gaban kasa.

Source: Facebook
A karshe, Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki, lalubo hanyar samaun kudaden shiga da zuba jari da zai samar da ayyukan yi.
Tinubu ya sa hannu kan dokar kare kudin kasa
A wani rahoton, kun ji cewa ana sa ran cewa sabuwar dokar da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu, za ta kara wa asusun rarraba kudi na kasa karfi.
Dokar ta yi tanadin cewa dole ne a mayar da dukkanin riba da harajin fetur kai tsaye ga baitul-mali, wanda ake kasafta wa tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.
Ana sa ran tasirin wannan sauyi zai bayyana a taron FAAC na gaba, yayin da gwamnati ke jaddada manufar 'Najeriya a kan gaba' wajen kare kudin kasa.
Asali: Legit.ng

