Tsaro Ya Damalmale, Amnesty Ta Fadi Yawan Mutanen da aka Sace a Watanni 3

Tsaro Ya Damalmale, Amnesty Ta Fadi Yawan Mutanen da aka Sace a Watanni 3

  • Kungiyar da ke rajin kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce lamarin tsaro ya kara dagulewa musamman a jihohin da ke Arewacin Najeriya
  • Kungiyar ta bayyana haka ne bayan ta fitar da alkaluma game da adadin mutanen da ake da tabbacin yan bindiga sun yi garkuwa da su a cikin watanni uku
  • Amnesty Int'l ta bayyana cewa hare-haren sun kara tsananta tare da kisan kai, sace-sace da cin zarafin jama’a a sassa daban-daban na kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty Int'l ta bayyana cewa Najeriya na fuskantar mummunar matsalar sace mutane da ke kara tabarbarewa.

Ta bayyana cewa alkalumanta sun tabbatar mata da cewa an sace akalla mutane 1,100 a jihohin Arewa tsakanin Janairu zuwa Afrilu 2026.

Kara karanta wannan

An kama ɗan shekara 15 da ake zargi da hannu a kashe Janar a harin Borno

An samu karuwar rashin tsaro a Najeriya
Hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Shaaibu, Bola Ahmed Tinubu Hoto: HQ Nigerian Army/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Kungiyar ta tabbatar da haka ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, inda ta ce wannan matsala ta kai wani mataki mai hatsari.

'Matsalar tsaro ta yi kamari' - Amnesty Int'l

Jaridar Thisday ta ruwaito a cewar Amnesty Int'l ‘yan bindiga ke kai hare-hare kan kauyuka da sansanonin ‘yan gudun hijira, suna kashe mutane tare da sace wasu da dama.

Ta ce wadanda ake sacewa suna fuskantar azaba, yunwa, fyade da sauran munanan halaye yayin da suke tsare ana jiran su biya kudin fansa.

Ta kara da cewa yawan hare-haren ya bazu a jihohi da dama, wanda ke nuna cewa lamarin ya fi yadda ake gani a bayan an yi kididdiga.

Amnesty ta shawarci gwamnati ta duba matsalar tsaro
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto; Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugaban kungiyar a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce ‘yan bindiga na kara tsananta farmaki kan al’ummomi masu rauni, suna hada kisan kai da sace mutane domin samun kudi.

Rahoton ya kuma bayyana wasu manyan hare-hare da suka faru a jihohi daban-daban, daga ciki har da harin da wanda aka kai Woro a jihar Kwara inda aka kashe mutane kusan 200 tare da sace 176.

Kara karanta wannan

Dalilin gwamnan Borno na goyon bayan harin sojin sama duk da rasa rayuka akalla 200

Amnesty: Hare-haren da aka kai jihohi

A jihar Zamfara, an sace mata da yara 150 a kauyukan Kurfa Danya da Kurfan Magaji, yayin da a Borno aka sace fiye da mutane 100 a dajin Kumbul.

A Kaduna da Neja ma an samu hare-hare da dama da suka shafi daruruwan mutane. Amnesty ta ce ana kai wadannan hare-hare da kone-kone da barnar dukiyoyi.

Ta bayyana cewa lamarin yana tilasta wa iyalai sayar da kayayyaki ko tara kudin daga al’umma domin fansar ‘yan uwansu. Wadanda ba su iya biyan fansa ba kuwa suna cikin masifa.

Amnesty ta yi magana kan hukuncin kisa

A baya, mun wallafa cewa kungiyar da ke rajin kare haƙƙin bil’adama ta duniya, Amnesty Int’l, ta sake sabunta kiran ta ga gwamnatin Najeriya a kan hukuncin kisa da ake yanke wa a jihar.

Kungiyar ta bukaci mahukuntan Najeriya da su soke duk wata doka da ke tanadin hukuncin kisa a kasar Ƙungiyar ta yi wannan kira ne a wani taro da ta shirya tare da haɗin gwiwar jakadancin Faransa a Abuja.

An bayyana cewa a ce babu wata hujja da ke tabbatar da cewa hukuncin kisa yana rage aikata manyan laifuffuka, saboda haka ta bukaci a soke shi domin samar da wata hanya ta hukunta masu laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng