Amnesty Int'l Ta Bukaci Gwamnati Ta Soke Hukuncin Kisa a Najeriya
- Amnesty Int’ ta bukaci mahukuntan Najeriya da su soke duk wata doka da ke tanadin hukuncin kisa a kasar
- Ƙungiyar ta yi wannan kira ne a wani taro da ta shirya tare da haɗin gwiwar jakadancin Faransa a Abuja
- An bayyana cewa a ce babu wata hujja da ke tabbatar da cewa hukuncin kisa yana rage aikata manyan laifuffuka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Abuja – Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta duniya, Amnesty Int’l, ta sake sabunta kiran ta ga gwamnatin Najeriya a kan hukuncin kisa.
Wannan na zuwa a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a birnin Abuja domin tunawa da Ranar Yaƙi da Hukuncin Kisa ta Duniya.

Source: Facebook
BBC Hausa ta wallafa cewa Manajar shirye-shirye na Amnesty a Najeriya, Mrs Barbara Magaji, ce ta bayyana haka yayin jawabi a taron.

Kara karanta wannan
Hana El Rufai taro: Kotu ta umarci 'yan sanda su biya jam'iyyun adawa diyyar N15m
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amnesty Int’l ta shawarci Najeriya
Mrs Barbara Magaji ta bayyana cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta bi sahun sauran ƙasashe da suka cire hukuncin kisa daga tsarin shari’arsu.
Taron dai ya samu haɗin gwiwar ofishin jakadancin Faransa a Najeriya, inda aka tattauna hanyoyin da za a bi don kawar da hukuncin kisa daga cikin tsarin shari’arsu.

Source: Facebook
A cewar Mrs Magaji, babu wani bincike ko shaidar da ke nuna cewa hukuncin kisa yana hana aikata manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, fashi, ko kisan kai.
A maimakon haka, ta ce ana ci gaba da samun karuwar laifuffuka duk da tanadin wannan hukunci a dokokin ƙasar.
Ta ce:
“Akwai jihohi 26 da birnin tarayya Abuja da ke da dokokin da ke tanadar da hukuncin kisa ga laifuffukan da suka haɗa da garkuwa da mutane, fashi, satar shanu da kuma laifuffukan tsafi. Amma duk da haka, irin waɗannan laifuffukan na ƙara yawaita kullum.”
Amnesty ta nemi a soke hukuncin kisa
Manajar shirye-shirye na Amnesty a Najeriya, Mrs Barbara Magajita ta kuma bukaci majalisar dokokin ƙasa ta duba yiwuwar soke duk wata doka da ke tanadin hukunci.
A cewarta, duniya na tafiya ne zuwa ga kare rayuwar ɗan adam ta hanyar kawo sauyi a tsarin hukunci, kuma bai kamata a bar Najeriya a baya ba.
Ta jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta rungumi sauyi domin kare haƙƙin rayuwa da inganta tsarin shari’a a Najeriya.
Ana murkushe masu zanga-zanga - Amnesty
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya, Amnesty International, ta bayyana damuwar ta matuƙa dangane da yadda jami’an tsaro ke murkushe zanga-zanga.
Ta yi zargin cewa jami'an sun murkushe masu zanga-zanga a birane irin su Abuja da Fatakwal inda ta ce an ci zarafin ‘yan jarida da sauran masu bayyana ra'ayinsu a jihohi.
Amnesty ta yi kira da a gudanar da bincike a kan waɗannan kame domin gano gaskiya da hukunta waɗanda laifi wajen dakile hakkokin jama'a wacce dokar Najeriya ta ba su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
